An gurfanar da mutumin da ya yi wa akuya 'fyade'

An gurfanar da mutumin da ya yi wa akuya 'fyade'

An gurfanar da wani mutum mai shekaru 22, Sunday Ogaji a gaban kotun gargajiya da ke zamanta a Ado Ekiti kan zargin yi wa akuya fyade.

Rundunar yan sanda ta na tuhumar Mista Ogaji da laifin aikata dabi'ar da ta saba wa al'adar ɗan adam.

Lauyan mai shigar da ƙara, sajan ɗan sanda, ya shaidawa kotu cewa wanda aka yi karar ya aikata laifin ne a ranar 4 ga watan Maris misalin ƙarfe 2.30 na rana a unguwar Basiri a Ado Ekiti.

An gurfanar da mutumin da ya yi wa akuya 'fyade'

An gurfanar da mutumin da ya yi wa akuya 'fyade'
Source: Twitter

Ya yi zargin cewa wanda aka yi karar ya yi wa akuyar fyade kuma ta mutu nan take.

Mista Apata ya ce laifin ya saba wa sashi na 214 (2) na dokar masu aikata laifi na jihar Ekiti na shekarar 2012.

Mai shigar da karar ya bukaci kotu ta dage sauraron shari'ar domin bashi damar gabatar da shaidu.

Wanda aka yi karar ya musanta aikata laifin.

DUBA WANNAN: Hotunan ganawar Sanusi II da El-Rufai a garin Awe

Lauyan sa, Timi Omotosho ya roki kotu ta yi wa wanda ya kare wa sassauci.

Shugaban kotun, Kehinde Awosika ya bayar da belin wanda aka yi karar kan kudi N50,000 da mutum daya da ya tsaya masa.

Ta dage cigaba da sauran shari'ar zuwa ranar 31 ga watan Maris kamar yadda NAN ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel