Yanzu-yanzu: An kebe Cristiano Ronaldo kan tsoron ya kamu da cutar Coronavirus

Yanzu-yanzu: An kebe Cristiano Ronaldo kan tsoron ya kamu da cutar Coronavirus

Shahrarren zakaran dan kwallo, Cristiano Ronaldo, ya kebe kansa a gidansa dake Madeira bayan an tabbatar da cewa abokin wasansa, Danielle Rugani, ya kamu da cutar Coronavirus.

Babban dan kwallon ya ziyarci mahaifiyarsa da ke fama da bugun jini a kasar Fotugal inda aka bayyana masa cewa yayi zamansa a gida kada ya koma Italiya da yake kwallo saboda cutar.

An kebe dan kwallon ne saboda ya zauna daki daya da Danielle Rugani a ranar Lahadi bayan wasansu da Inter Milan da sukayi babu yan kallo.

Hoton da dan wasa Miralem Pjanic ya daura a Instagram bayan wasan ya nuna Ronaldo da Rugani suna runguman juna.

Dukkan wadanda suka hada jiki da Rugani a ranar an killacesu. Hakazalika an dakatad da wasannin Serie A zuwa ranar 3 ga Afrilu.

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel