Yanzu-yanzu: An dauke Sanusi Lamido daga Loko, za a mayar da shi Awe

Yanzu-yanzu: An dauke Sanusi Lamido daga Loko, za a mayar da shi Awe

Rahoto daga majiya mai karfi ya tabbatar mana da cewa an shirya tsaf domin dauke tubabben sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu, daga kauyen Loko zuwa karamar hukumar Awe, ta jihar Nasarawa.

Shugaban maaikatan tsohon sarkin, Munir Sanusi, ya bayyawa DN cewa sun dira gidan gwamnatin jihar yanzu domin garzayawa Awe.

Hakazalika, kwamishanan yan sandan jihar, Bola Longe, da shugaban hukumar DSS na jihar, suna gidan gwamnatin domin tarban Sanusi.

An tattaro cewa garin Loko bata kamaci Sarki Sanusi ba kuma Awe ta fi zama cikin gari da kayan jin dadin rayuwa.

Ku saurari cikakken rahoton.....

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel