Banda bautar Allah, jima'i shine abinda yafi komai muhimmanci a rayuwa - Jaruma Juliet Njemanze

Banda bautar Allah, jima'i shine abinda yafi komai muhimmanci a rayuwa - Jaruma Juliet Njemanze

- Kyakyawar jarumar masana’antar Nollywood, Juliet Njemanze wacce tayi suna a fim dinta mai suna Calabash ta bayyana wasu sirrika game da rayuwarta

- Jarumar ‘yar asalin jihar Imo din ta bayyana matsayarta a kan jima’i, soyayya da kuma zamantakewa

- Ta ce daga Ubangiji sai jima'i sune kan gaba a rayuwarta kuma ko kudin duk duniya namjin zai ba ta matukar bashi da kwazo za ta ci amanarshi

Kyakyawar jarumar masana’antar Nollywood, Juliet Njemanze wacce shahararta ta biyo bayan rawar da ta taka a shirin nan mai suna “Calabash” ba ta cika sassautawa ba idan aka yi maganar soyayya, rayuwa, zamantakewa da kuma ra’ayi.

Jarumar ‘yar asalin jihar Imo din wacce ita kadai mace iyayenta suka haifa a cikin ‘yan uwanta maza hudu, ta bayyana matsayarta a kan jima’i, soyayya da kuma zamantakewa.

“A gareni, daga ubangiji sai jima’i ne mafi muhimmanci a wajena. Dole ne namiji ya zama jarumi a shinfida. Jima’i ne farkon komai kafin kudi ya biyo baya. Koda namiji zai bani duk kudin duniyar nan, zan ci amanar shi idan bai iya komai a gado ba.” Ta sanar yayin da aka tambayeta don zaba tsakanin soyayya, kudi da jima’i.

Banda bautar Allah, jima'i shine abinda yafi komai muhimmanci a rayuwa - Jaruma Juliet Njemanze

Banda bautar Allah, jima'i shine abinda yafi komai muhimmanci a rayuwa - Jaruma Juliet Njemanze
Source: Twitter

KU KARANTA: Sarkin maroka: Mabaracin da ya mallaki gidaje biyar, motoci 20 da kamfanin ruwan leda

Amma a lokacin da aka tambayeta ko akwai irin rawar da za ta iya takawa a fina-finai na jima’i, sai ta ce ba za ta taba iyawa ba don zai taba mutuncinta.

Akwai rawar da ba zan iya takawa ba kuma ba zan iya fitowa ba. Idan lamarin na bukatar batanci ko fadin wani abu da zai girgiza imani na, ba zan iya ba. Zan iya runguma da abubuwan da suka danganci soyayya amma banda jima’i a wasan kwaikwayo.” Ta ce.

"Ina kaunar Ubangiji kuma ina karanta littafi mai tsarki. Ba dole in je coci kowacce lahadi ba amma ina kiyaye addinina.” Ta ce.

A yayin da take kwatanta halayen nagartarta, ta ce tana da gaskiya da rikon amana kuma bata karya da yaudara.

Juliet ta fara wasan kwaikwayo ne a 2013 inda ta fara bayyana a fim mai suna “Tears in my heart” kafin tayi fim din da ta shahara a 2015 mai suna “Calabash”.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel