KAI TSAYE: Masu nada sabon sarki sun isa gidan gwamnatin Kano (Hotuna da bidiyo)
1 - tsawon mintuna
Bayan tube rawanin Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje yayi, masu alhakin nada sabon sarki a jihar Kano sun hallara a fadar Gwamna Ganduje da ke Kano.
Tuni dai jami'an tsaro suka yi awon gaba da tuabbaben Sarkin inda za a fitar da shi daga jihar ta Kano baki daya.
Masu alhakin nada sabon sarkin sun hada da: Madakin Kano, Yusuf Nabahani, Makaman Kano; Sarki Abdullahi, Sarkin Dawaki Mai Tuta, Abubakar Tuta, Sarkin Bai, Mukhtar Adnan.
Asali: Legit.ng
Tags: