Kwararon robar wadanda suka kwanta damu muke kaiwa bokaye - Karuwai

Kwararon robar wadanda suka kwanta damu muke kaiwa bokaye - Karuwai

- Jami’an ‘yan sanda a Najeriya sun kama wasu dalibai mata hudu na jami’a dauke da kwaroron roba da ke kunshe da maniyyi a ciki

- Daliban hudu duk ‘yan makaranta ne ta gaba da sakandare a jihar Akwa Ibom kuma an kama su ne sakamakon bayanan sirri da ‘yan sandan suka samu

- Ta ce hausawan da ke siya suna kaiwa Alhazawan Abuja da Legas ne wadanda suke yin duk tsafin da suke bukata da shi

Jami’an ‘yan sanda a Najeriya sun kama wasu dalibai mata hudu na jami’a dauke da kwaroron roba da ke kunshe da maniyyi a ciki.

Daliban hudu duk ‘yan makaranta ne ta gaba da sakandare a jihar Akwa Ibom kuma an kama su ne sakamakon bayanan sirri da ‘yan sandan suka samu dangane da daliban.

Daliban masu karantar fannin karatun jarida a makaranta, sun bayyana cewa suna karuwanci don suna kwanciya da maza kala-kala. Bayan kwanciya kuwa da mazan, suna daukar kwararon robar da suka yi amfani da shi don siyarwa da hausawa a jihar da tsada.

Kwararon robar wadanda suka kwanta damu muke kaiwa bokaye - Karuwai

Kwararon robar wadanda suka kwanta damu muke kaiwa bokaye - Karuwai
Source: Facebook

KU KARANTA: Na dauka mintuna 45 don tabbatar da mutuwarta - Saurayin da ya soka wa budurwa wuka

Kamar yadda ‘yan matan suka sanar, sun fada wannan kasuwancin ne tun kusan shekaru uku da suka gabata bayan sun fara karatu.

Glory Edet, daya daga cikin ‘yan matan ta ce a kowanne lokaci ta kwanta da namiji, da kanta take cire kwararon robar da nufin ta damu da namijin. Daga nan sai tayi tamkar za ta yadda shi amma sai ta kulle shi a leda ta jefa a jakarta.

Ta ce hausawan da ke siya suna kaiwa Alhazawan Abuja da Legas ne wadanda suke yin duk tsafin da suke bukata da shi.

Kamar yadda suka ce, sa’arsu ta zo karshe ne bayan da makwabciyarsu ta ji da yadda suke rayuwa sannan ta kaiwa ‘yan sanda rahoto.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel