Innalilahi: Bidiyon wani mutum da aka kama yana lalata da akuya a cikin kango

Innalilahi: Bidiyon wani mutum da aka kama yana lalata da akuya a cikin kango

Mazauna Owode Quarters a Ado Ekiti na jihar Ekiti sun sha mamaki bayan an kama wani yaro mai suna Peter David yana lalata da wata akuya mai juna biyu a wani kangon gini a unguwar.

An kama David ne sakamakon ihun da akuyar ke yi da ya janyo hankulan mazauna unguwar da ma'aikatan hukumar rarraba wutan lantarki na Benin, BEDC, a safiyar ranar.

Mazauna unguwar sun ce akuyar da kwashe kimanin awanni biyu kumfa na fita daga bakin ta kuma jini na zuba daga al'uarar ta.

'Yan sanda daga bisani sun zo sun dauke yaron da akuyar kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Wata mata da ke zaune a unguwar, Misis Oluwosola da ta ce jami'an hukumar wuta, BEDC, ne suka sanar da ita sannan ita kuma ta kira wasu mutane su shaida abinda ta kira abin kunya.

DUBA WANNAN: An dage auren Suleiman Panshekara da masoyiyarsa 'yar Amurka

Misis Ayodele ta ce ta kira wasu su taimaka mata yayin da mutumin ke kokarin tserewa ta rafin Ofin zuwa garin Ifeoluwa amma wani Fasto Gbenga Ajulo ya damko shi.

Ajulo wanda fasto ne a Christ Apostolic Church, Throne of Mercy da ke Owode ya ce yana addu'a ne a coci amma ya ke jin kukan akuyar babu kakautawa.

Shugaban karamar hukumar garin Ifeoluwa, Mista Abel Bankole ya bayyana abin a matsayin abin mamaki da tsoro ya kuma ce a yi wa mutumin gwaji a asibiti.

Ya kara da cewa, "Akwai yiwuwar ya kamu da cuta. Cutar da zai iya yadawa idan ya sadu da wasu."

Kakakin 'yan sandan jihar Ekiti, Sunday Abutu ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda ya ce jami'an sashin 'Yaki da Fashi da Makami' sun kama wani mutum da ke zina da akuya a unguwar.

"An masa tambayoyi kuma ya amsa cewa ya aikata laifin. Ya kuma ce dama yana aikata hakan kafin ya zo jihar Ondo. Muna cigaba da masa tambayoyi kan dalilin da yasa ya ke aikata hakan. Akwai yiwuwar a gurfanar da shi."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel