Masoya biyu sun mutu bayan sun sha maganin kara armashin jima'i sun kwana suna zina

Masoya biyu sun mutu bayan sun sha maganin kara armashin jima'i sun kwana suna zina

- Wasu masoya biyu sun sheka lahira a dakin su da ke titin Elechi-Wobo a Fatakwal da ke jihar Ribas

- An zargi cewa masoyan biyu sun mutu ne bayan dirkar magungunan karin armashin jima’i

- An same su ne tsirara a dakinsu din amma kuma mazakutar saurayin a tsaye kyam

Wata mata da masoyinta wadanda ba a san ko su waye ba an samu gawawwakinsu a dakinsu. Ana zargi cewa masoyan biyu sun mutu ne bayan dirkar magungunan karin armashin jima’i a garin fatakwal da ke jihar Ribas.

An samu gawar macen tare da saurayinta ne wanda mazakutarsa ke tsaye a wani gidan bene da ke titin Elechi-Wobo a Fatakwal, kamar yadda jaridar The Nation Online ta ruwaito.

Ganau ba jiyau ba, sun ce makwabtansu ne suka balle dakin inda suka tarar da gawawwakinsu tsirara.

“Mamacin ya samu babbar sallama daga wajen ubangidansa a watan Fabrairun da ya gabata bayan hidimta masa da ya dinga yi a Ikoku. Tuni kuma ya fara shirin auren budurwar ta shi. An samu magungunan karin armashin saduwar a teburin da ke kusa da katifarsu,” kamar yadda wani ganau ya fadi.

Bayan shan maganin armashin jima'i, saurayi da budurwa sun mutu bayan suna lalata

Bayan shan maganin armashin jima'i, saurayi da budurwa sun mutu bayan suna lalata
Source: Twitter

DUBA WANNAN: An dage auren Suleiman Panshekara da masoyiyarsa 'yar Amurka

Mutumin dai bai karasa mutuwa ba har sai da aka danganta da asibiti kuma ya kwashe kwanaki uku kafin ya rasu.

An tuntubi rundunar ‘yan sandan jihar Ribas din kuma har yanzu ba su mayar da martani a kan lamarin ba.

Idan za mu tuna, Legit.ng ta ruwaito yadda wani mutum mai matsakaicin shekaru ya mutu a dakin otal.

Bayan ya karba dakin daga hukumar otal din tare da budurwarsa wacce suka je tare ne sai fito bayan kankanin lokaci tana ihun neman taimako.

Kamar yadda rundunar 'yan sanda ta bayyana, babu alamun fada ko wani abu a tattare da gawar amma an samu maganin karin karfin maza a dakin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel