An yi wa matar basarake da surukarsa fyade

An yi wa matar basarake da surukarsa fyade

- Mata uku ne wadanda suka hada da matar dagaci da surukansa biyu 'yan bindiga suka yi wa fyade a ranar Alhamis a jihar Benue

- 'Yan bindigar sun kai hari kauyen ne da sa'o'in farko na ranar Alhamis inda suka zagaye gidan basaraken

- Ya tabbatar wa da manema labarai cewa 'yan bindigar sun kashe musu wasu dabbobi sannan suka yi awon gaba da wasu daga ciki

Mata uku ne wadanda suka hada da matar dagaci da surukansa biyu ne ‘yan bindiga suka yi wa fyade a sa’o’in farko na ranar Alhamis, bayan harin da suka kai yankin Mbanyiar da ke karamar hukumar Guma ta jihar Binuwai.

Jaridar daily Trust ta gano cewa maharan sun bayyana ne da miyagun makamai kuma sai suka zagaye gidan basaraken sannan suka yi wa matarsa fyade da surukansa mata biyu.

An yi wa matar basarake da surukarsa fyade

An yi wa matar basarake da surukarsa fyade
Source: Twitter

Basaraken, wanda ya bukaci da a sakaya sunansa, ya sanar da manema labarai cewa ana zargin maharan Fulani ne makiyaya don har kayan abincinsu sai da suka lalata a yayin harin.

Ya bayyana cewa maharan su 11 ne kuma sun iso ne wajen karfe 2 na dare, amma ya samu nasarar tserewa daga garesu.

DUBA WANNAN: Bidiyon dan sanda da ya daka tsalle ya dare kan motar da ke gudu a titi don ya tsayar da direban

Ya ci gaba da bayyana cewa maharani sun je yankin a makon da ya gabata inda suka kashe musu dabbobin da suka hada da akuya, aladu da kuma kaji, yayin da suka yi awon gaba da wasu.

“Tun daga aukuwar lamarin, ban kara ganin matata ba da sirikaina mata biyu. Amma mai gadin dabbobin ya ce ana ta azabtarwa tare da yi musu fyade amma ba a kashe su ba. Na kai kara ofishin ‘yan sanda,” yace.

Har dai a halin yanzu, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Benue din, Catherine Anene, ta ce ba ta samu wani rahoto a kan hakan ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel