Tirkashi: Saurayi ya yiwa budurwarshi tsirara a cikin jama'a saboda taki yadda ta aure shi

Tirkashi: Saurayi ya yiwa budurwarshi tsirara a cikin jama'a saboda taki yadda ta aure shi

- Wani bidiyon masoya biyu da lamarin soyayyarsu ya watse ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumuntar zamani

- A bidiyon dai an ga saurayin ya durkusa kasa yana neman amincewar budurwa shi don aurenshi a cikin wani wajen cin abinci mai cike da jama’a

- Bayan kin amincewarta ne ya tashi a fusace inda ya juye abincin da ya siya mata a leda tare da kwace takalmin da ke kafarta don ya ce shi ya siya

Ka kwatanta yadda za ka ji idan mace ta nuna rashin son ka fili kuma cikin bainar jama’a. A yayin da kayi kokarin bayyana mata burinka na aurenta a wajen cin abincin da ke cike da mutane amma ta ki aminta da kudirinka.

Wani abin kunya da bada haushi ne ya faru da wani matashi wanda ya bukaci budurwar shi ta aure shi a gaban jama’a amma ta nuna bata amince ba. Tuni fusataccen saurayin ya tube mata takalman da ke kafarta don a cewar shi, shi ya siyo su.

Kafin cire mata takalman, fusataccen matashin sai da ya fara juye abincin da ya siya mata a cikin leda baka.

Bayan ya karbe kayayyakin shi, sai ya fice daga wajen cin abincin a fusace, kamar yadda jaridar Pulse.ng ta wallafa.

KU KARANTA: A dinga barin mata suna auren maza biyu ko da za a samu akasi daya ya mutu - Jarumar fim

Kamar yadda bidiyon ya nuna, an gano cewa saurayin da budurwar sun dade suna soyayya amma sai saurayin yayi tunanin ya kamata su kai wani mataki a soyayyar. Bai kuma taba tsammanin cewa budurwar na da wani tunanin da ba hakan ba.

Budurwar kuwa ta sha mamaki da yadda saurayin nata ya yi martanin abinda tayi mishi, don kuwa ta kasa cewa komai balle ta iya tashi daga kujerar da take.

Tuni dai bidiyon masoyan biyu ya yi yawa a yanar gizo kuma mutane daban-daban na ta yin tsokaci a kan hakan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel