Yanzu-yanzu: Saudiyya ta dakatad da aikin Umrah gaba daya

Yanzu-yanzu: Saudiyya ta dakatad da aikin Umrah gaba daya

Gwamnatin kasar Saudiyya ta dakatad da aikin Umrah da ziyarar Masallacin Annabi mai girma ga dukkan yan kasar da mazauna sakamakon bullar cutar Coronavirus a kasar.

Ma'aikatar kiwon lafiyar kasar ta dau matakin ne domin takaita yaduwar cutar a kasar mai alfarma.

Shugabancin Masallacin Harami karkashin jagorancin babban limami, Sheikh Abdur-Rahman As-Sudais ta kaddamar da feshi da tsaftace Mataaf na musamman domin kawar da yaduwar cutar Corona.

Mabiya addinin Islama a fadin duniya sun yi mamakin hakan inda da dama suka ce wannan shine karo na farko da zasu ga Masallacin Harami babu kowa.

Source: Legit

Tags:
Online view pixel