Matasa sun yiwa budurwa 'yar madigo fyade domin su gyarata ta fara son maza

Matasa sun yiwa budurwa 'yar madigo fyade domin su gyarata ta fara son maza

- Matasa sun yiwa wata budurwa 'yar madigo fyade a kasar Afrika ta Kudu, inda suka ce sunyi hakane don su daidaita ta ta fara son maza

- Mazan guda uku sun kama budurwar a lokacin da take kan hanyarta ta zuwa wani shago

- Jami'an tsaro sun samu damar cafke biyu daga cikin masu laifin dayan kuma ya gudu

'Yan sanda sun kama wasu matasa guda biyu masu shekaru 17 da 14 da laifin yiwa wata mata fyade a kasar Afrika ta Kudu.

Matasan guda biyu sun yiwa matar mai shekaru 25 fyade wacce take 'yar madigo ce a cikin wani wuri a karshen makon da ya gabata.

A rahoton da Daily Voice ta bayar mutane uku ne ake zargi da yiwa matar wannan aika-aika domin su gyara ta ta fara son maza.

Matasan sun yiwa budurwar fyade kwana daya kafin a gabatar da wani gagarumin biki a birnin Cape Town a ranar Asabar dinnan da ta gaba, wanda ake yin shi akan 'yancin masu auren jinsi, da kuma wayar da kan mutane kan auren jinsi.

Da yake bayani akan lamarin, kwamandan ofishin 'yan sandan na Grassy Park, Colonel Dawood Laing, wanda yayi bayani a ranar Juma'a, matar tana kan hanyarta ta zuwa wani shago, a lokacin ne matasan suka kai mata hari.

Laing ya ce daya daga cikin matasan ya sanya hannunshi a wuyan matar ya gaya mata cewa yana so yayi amfani da ita ne.

Sun yi mata kaca-kaca, sai ta gudu gida, amma 'yan gidansu duk sun yi bacci dole yasa ta hakura sai da safiyar ranar Asabar suka kai karar abinda ya faru ga 'yan sanda.

A cewar Laing, mutanen yankin da 'yan sanda sun shiga tashin hankali dalilin wannan abu, kuma ya bayyana cewa za su yi iya bakin kokarinsu wajen gano mutum na uku da yake da hannu a lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel