Jami'ar Moddibo Adama ta sallami manyan malamai 2 kan lalata da daliba

Jami'ar Moddibo Adama ta sallami manyan malamai 2 kan lalata da daliba

Majalisar zantarwan jami'ar Moddibo Adama dake Yola, babbar birnin jihar Adamawa ta sallami manyan malamanta biyu kan laifin lalata da wata dalibar makarantan.

Wannan labari na kunshe cikin jawabin da jami'in yada labaran Jami'ar, Aminu Gururmpawo, ya sai ranar Talata a Yola.

Hakazalika Aminu Gururmpawo ya kara da cewa jamiar ta sallami wani alhaj Bakari Girei na sashen rajista kan laifin almundahanan kudin kungiyar malamai da iyayen makarantar firamaren jamiar, kimanin N1.12 million.

Yace: “Majalisar zantarwar Jami'ar Moddibo Adama dake Yola a ganawarta na 96 da aka yi ranar alhamis, 27 ga Febrairu 2020 ta tabbatar da sallamar manyan ma'aikatan jami'ar uku.“

“An sallami manyan malamai biyu ne kan laifin cin mutunci da lalata.“

“ Sune na Dr Yakubu Bobboi da Dr Toma Fulani Mbahi na tsangayar ilimin dabbobi kuma an ladabtar da su ne kan bita da kulli da kokarin lalata da wata dalibar majistir mai suna, C.A Bathon.“

“Yayinda shi kuma Alhaji Mohammed Bakari-Girei, mataimakin rejisran, aka sallamesa kan laifin rub da ciki da kudin kungiyar malamai da iyayen makarantar firamaren jamiar, kimanin N1.12 million.“

Jami'ar Moddibo Adama ta sallami manyan malamai 2 kan lalata da daliba

Jami'ar Moddibo Adama ta sallami manyan malamai 2 kan lalata da daliba
Source: UGC

A wani labarin daban, Jami'ar jihar Kaduna KASU ta bayyana cewa ta sallami daliban makarantar 80 kan laifin satar amsa a kakar 2018/2019 da ya gabata.

Shugaban gidan karatun Kafanchan, Farfesa Ahmed Ahmed, ya bayyana hakan ne a ranar Laraba wajen taron maraba da rantsar da sabbin daliban da suka samu shiga jamiar a sabuwar kakar 2019/2020.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ta ruwaito cewa an gudanar da taron maraba ga sabbin daliban a sassan Jami'ar biyu na Kaduna da Kafanchan a lokaci guda.

Farfesa Ahmed ya bayyana cewa daga cikin dalibai 80 da Jami'ar ta sallama, 10 daga cikinsu yan sashen Kafanchan ne kuma abin takaici ne dubi ga yadda ana rububin nemar shiga Jami'ar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel