Yadda mace mai shekaru 70 ta yi wa mafarauta jagora tsirara suka shiga daji suka kashe 'yan bindiga 40 a Neja

Yadda mace mai shekaru 70 ta yi wa mafarauta jagora tsirara suka shiga daji suka kashe 'yan bindiga 40 a Neja

Wata mata mai shekaru 70, a karshen makon da ya gabata ta jagoranci tawagar 'yan banga tsirara sun shiga daji sun yi maganin wasu yan bindiga da ke addabar wasu kananan hukumomi a jihar Neja inda suka lashe a ƙalla 'yan bindiga 40.

Bayan kashe yan bindigan an gano cewa sun kwato manyan makamai daga hannun 'yan bindigan bayan fafatawa da su kayi a karamar hukumar Zugurma Mashegu a jihar.

An ruwaito cewa jagorar su 'mace' ta shafa wa yan bangan wasu magungunan gargajiya a kafarsu kafin ta musu jagora suka shiga dajin na Zugurma inda ta ce su yi harbi domin 'yan bindigan da ke boye a dajin su fito.

Wata majiya ta ce 'yan bindigan sun fito daga inda suka boye suna harbi amma ba su ga matan ba da 'yan bangan.

Yadda mace mai shekaru 70 ta yi wa mafarauta jagora tsirara suka shiga daji suka ragargaji 'yan bindiga a Neja

Yadda mace mai shekaru 70 ta yi wa mafarauta jagora tsirara suka shiga daji suka ragargaji 'yan bindiga a Neja
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Ba na nadamar datse min hannu da shari'a ta yi - Dan jihar Zamfara

Hakan yasa mafarautan suka bi sahun 'yan bindigan inda suka damke a ƙalla 40 daga cikinsu yayin da wasu suka tsere kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Wani kwararar majiya daga unguwar ya ce an umurci kwanan 'yan bindigan da ya boye a kan bishiya ya sako kuma aka kama shi yayin da wasu 'yan bindigan da suka shiga cikin gari siyo katin waya da wasu kayan masarufi suma an kama su an mika wa yan sanda.

Mafarautan sun shaida wa wasu 'yan kauyen cewa ba su kashe shugaban yan bindigan bane saboda suna son ya bawa yan sanda bayanai kan yadda za a kamo sauran.

Rundunar yan sandan jihar ba ta ce komai a kan lamarin ba yayin da wani babban ɗan sanda ya ce an tura jami'ai su tafi dajin domin bin sahun yan bindigan da nufin kamo sauran.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel