An kama daraktan kudi da abokan aikinsa guda biyu kan lalata da 'yar shekara 12 a jihar Sokoto

An kama daraktan kudi da abokan aikinsa guda biyu kan lalata da 'yar shekara 12 a jihar Sokoto

- Hukumar hana fataucin mutane ta kasa a ranar Talata, ta ce ta gurfanar da wasu manyan jami'an jahar Sokoto su uku

- Ana zargin su ne da lalata da wata yarinya 'yar shekara 12 da ke siyar da ruwan leda

- Yarinyar dai ta je neman taimako na kudi ne a wajensu inda suka yi amfani da hakan wajen haike mata

Hukumar hana fataucin mutane ta kasa a ranar Talata, ta ce ta gurfanar wani daraktan kudi mai shekara 45 a hukumar tsare-tsaren birane da yankuna na jahar Sokoto, Ahmed Yahaya da wasu ma’aikatan hukumar biyu a gaban kotu bisa zargin lalata da wata yarinya yar shekara 12 da ke tallar ruwan leda.

Jami’in labarai na NAPTIP, Mista Vincent Adekoye, a wani jawabi, ya bayyana sauran masu laifin biyu a matsayin mai binciken kudi na gwamnatin jahar Sokoto, Mista Ibrahim Isah mai shekara 46, da mataimaki na musamman ga daraktan kudi, Mista Habibu Abdullahi mai shekara 40.

An kama daraktan kudi da abokan aikinsa guda biyu kan lalata da 'yar shekara 12 a jihar Sokoto

An kama daraktan kudi da abokan aikinsa guda biyu kan lalata da 'yar shekara 12 a jihar Sokoto
Source: Twitter

A cewarsa, hukumar NAPTIP reshen Sokoto ta gurfanar da masu laifin a gaban wata babbar kotun tarayya da ke jahar Sokoto a shari’a mai lamba FHC/7c/2020,

Sai dai ya ce ba a riga an ba kowani alkali shari’an ba tukuna.

Adekoye ya ce cikakken bayanin shari’an ya bayyana cewa wani lokaci a Mayun 2019, wacce aka lalatar ta je ofishin wadanda ake zargin don neman taimako na kudi.

Ya kara da cewa wadanda ake zargin sun yi amfani da rashin gatar yarinyar sannan suka yi lalata da ita a lokuta mabanbanta a cikin ofishoshinsu.

Kakakin ya kara da cewa mutum na karshe da yi lalata da yarinyar shine Abdullahi, wanda bayan sanin cewa shugabansa baya nan, sai ya yaudari yarinyar zuwa cikin ofishinsa sannan ya yi lalata da ita, inda ya bata N300 daga bisani.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya rantsar da shugabannin hukumar da ke kula da Majalisa a Najeriya

Ya bayyana cewa hukumar ta kama wadanda ake zargin su uku kimanin makonni uku da suka gabata kan laifukan, bayan hukumar kare hakkin dan adam na kasa, ofishin jahar Sokoto sun tura lamarin zuwa gare su

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel