Innalillahi: Ana tilasta dalibai mata suna tsirara ana duba tsiraicinsu don a tabbatar da basa al'ada

Innalillahi: Ana tilasta dalibai mata suna tsirara ana duba tsiraicinsu don a tabbatar da basa al'ada

- Dalibai 68 a wata kwalejin mata da ke kasar India ne aka tirsasawa cire dan kamfan su don tabbatar da cewa basu jinin al’ada

- Daliban sun bayyana cewa an saba hantararsu tare da hukuntasu a duk lokacin da suke jinin al’ada

- Wannan al’ada ce a kasar India, a kan hana mata shiga madafi ko wajen bauta yayin al’ada don ana daukarsu a najasa ne

A kasar India, jinin al’ada abun kyama ne saboda tsanantar al’adun kasar. Ana kyamatar mace mai al’ada tare da cewa jikinta akwai najasa. Bayan nan, ana bukatar mace mai al’ada da kada ta shiga madafi, wajen bauta kuma ana bukatar su daina taba jama’a.

A farkon makon nan ne a jihar Gujarat da ke kasar India aka tirsasawa yara mata cire kamfan su don tabbatar da cewa basu al’ada bayan sun shiga madafi.

Innalillahi: Ana tilasta dalibai mata suna tsirara ana duba tsiraicinsu don a tabbatar da basa al'ada

Innalillahi: Ana tilasta dalibai mata suna tsirara ana duba tsiraicinsu don a tabbatar da basa al'ada
Source: Facebook

Kamar yadda daliban mata suka bayyana, wannan tozarcin an saba yi musu shi a kwalejin, jaridar Ahmedabad Mirror ta ruwaito.

Lamarin ya faru ne a makarantar ‘yan mata ta Shri Sahjanand, kwaleji ce da ta sadaukar da karatuttukanta wajen habakawa da tallafawa yara mata ta hanyar amfani da ilimin kimiyyya.

An bukaci yara matan 68 da su cire dan kamfan su don tabbatar da cewa ba al’ada suke ba bayan mai kula da dakin kwanansu ya zargesu da karya dokar addini.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Saudiyya ta bawa mata damar bude kungiyar kwallon kafa a kasar

Malamai mata ne suka sa daliban suka layi inda suka dinga duba su. “Hukumar kula da dakin kwanan ce ta zargemu tare da tozarta mu,” daya daga cikin daliban ta sanar.

“A ranar Alhamis, lokacin muna karatu sai Anjaliben ya kai wa shugaban makaranta karar mu cewa muna shiga madafi bayan muna al’ada. Hakan ne kuwa yasa suka sa muka yi layi aka dinga duba mu don tabbatar da ikirarinmu.” Ta kara da cewa.

An gano cewa wannan abu ya saba faruwa da daliban kwalejin Shri Sahjanand ta mata. “Ana hukunta mu idan muna jinin al’ada. Mun gaji da fuskantar wannan tozarcin. Bayan mun yi zanga-zanga sai shugaban makarantar ya ce zamu iya daukar matakin shari’a a kai. Ya tirsasa wasu daliban sun saka hannun cewa babu abinda ya faru.” Wata daliba ta ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel