Mata ta maka mijinta a kotu a kan ya kira ta da karuwa

Mata ta maka mijinta a kotu a kan ya kira ta da karuwa

Wata mata 'yar kasuwa mai suna Tina a ranar Laraba ta maka mijinta mai suna O. A Dickson a gaban wata kotun gargajiya da ke Nyanya da bukatar saki.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, Tina ta bukaci mjin nata ya sake ta ne a gaban kotun da ke birnin tarayya da ke Abuja a kan ya na kiranta da kalaman batanci da cin mutunci.

"Mijina yana kira na da sunayen cin zarafi. Yana kira da da bandakin kowa a gaban 'ya'yana. Ya saka min dokar ta-baci, kullum sai dai in dawo gida kafin karfe 6 na yamma," ta ce.

"Ina yawan rokon mijina da ya bar ni in kai dare a waje ballantana a ranakun da ma'aikata ke karbar albashinsu, saboda a cikin ranakun ayyuka sun fi yi min yawa. Na kan bi ofisoshi daban-daban a ranar don karbar bashin da aka ci na kayana. In ba haka ba, ba dole bane a biya ni bashi na." ta kara da cewa.

Mata ta maka miji a kotu a kan ya kira ta da karuwa

Mata ta maka miji a kotu a kan ya kira ta da karuwa
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Kotu ta aike wa shugaban gidan yari sammaci a kan hana El-Zakzaky ganin likita

Kamar yadda ta ce, "nayi juriya mai tarin yawa a wannan auren. Ya kira mahaifiyata da mayya. A tunani na wannan ne karshen abinda zan iya dauka. Ba zan iya ci gaba da wannan auren ba."

Wanda ake karar ya samu halartar zaman kotun amma ya musanta duk zargin da matarsa ke masa. Ya bukaci kotun da kada ta amshi bukatar matarsa din.

Alkalin kotun mai suna Shitta Muhammed ta shawarci ma'auratan da su sasanta kansu a gida. Ta dage sauraron karar zuwa ranar 2 ga watan Maris na 2020 don jin yadda suka kaya a sasancin gidan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel