Jami'an tsaro sun damke wani mutum a kan zargin yadda gawar masoyiyarsa a bakin hanya

Jami'an tsaro sun damke wani mutum a kan zargin yadda gawar masoyiyarsa a bakin hanya

Bangaren binciken manyan laifuka na rundunar 'yan sandan jihar Legas, sun fara binciken wani mutum da ake zarginsa da yadda gawar wata mata da ake zaton masoyiyarsa ce.

Wanda ake zargin mai suna Clement Ejindo na sana'ar siyar da kayan kwalliya ne kuma an kama shi ne ta bidiyon da ya yadu a kafafen sada zumuntar zamani, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

'Yan sandan sun je har wajen aikin shi na kanikanci inda abokin aikin shi ya kai jami'an har maboyarsa.

'Ya'yan matar sun sanar da 'yan sandan cewa, mutumin masoyin mahaifiyarsu ne kuma da kanshi ya kai motarta gida. Sun fara soyayya ne tun bayan mutuwar mijinta a shekaru hudu da suka gabata.

An zargi mutumin da zuba guba a ruwan gora kafin ya bata ta sha a ranar da ta mutu. An gano cewa da kanshi ya dauketa daga gidanta da ke Igando kafin ta hadu da mutuwarta.

A takardar da 'yan sandan suka sa hannu, sun ce wanda ake zargin ya sanar da cewa faduwa tayi a kan hanyarsu ta zuwa yankin Idimu da ke jihar Legas.

Ya ce mamaciyar na zaune a bayan motar ne inda ta fara tari kamar ta shake, bayan sun wuce babban asibitin Igando.

Jami'an tsaro sun damke wani mutum a kan zargin yadda gawar masoyiyarsa a bakin hanya

Jami'an tsaro sun damke wani mutum a kan zargin yadda gawar masoyiyarsa a bakin hanya
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Zamfara: Za a koma zaman majalisar jiha a makarantar firamare

"A lokacin da ta fara tari, na tambayeta ko tana bukatar ruwa sai ta ce eh. Na dau ruwa na bata amma sai ta sha kadan. Akwai cunkoson ababen hawa a titin amma haka na dinga bi har muka fita. Na tambayeta ko in kaita asibiti amma ban ji abinda take cewa ba," ya ce.

Ya kara da cewa, "na juya kan motar inda har na kai Isheri. Saboda cunkoson sai na bi wata karamar hanyar na ajiye motar. Amma nayi latti. Da kyar ta fito daga motar sai ta zauna a gefen titi. Wata mata da take wucewa ta tambayeni ko kadeta nayi, amma na sanar da ita ba hakan bane."

Ya ci gaba da cewa, "matar ta taimaka min wajen cire mata riga da rigar nono har dai zuwa lokacin da ta samu sauki muka ci gaba da tafiya. Mun kama hanyar Igando amma sai tarin ya dawo. Mun tsaya bakin titi inda wasu suka kawo mana taimako. A take ta fadi a mace, hakan kuwa yasa na gudu saboda tsoro."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel