Fyade: An yankewa malamin jami'a hukuncin shekaru 21 a gidan gyaran hali

Fyade: An yankewa malamin jami'a hukuncin shekaru 21 a gidan gyaran hali

Mai shari’a Josephine Oyefeso ta babbar kotun Ikeja da ke jihar Legas a ranar Alhamis ta yankewa Dr. Afeez Akin Baruwa hukuncin shekaru 21 a gidan gyaran hali. Wanda aka yanke wa hukuncin dai tsohon malamin jami’ar jihar Legas ne kuma ya samu wannan hukuncin ne sakamakon fyade da yayi wa wata yarinya mai shekaru 18 wacce ta je neman gurbin karatu a jami’ar.

Wanda aka yankewa hukuncin na da shekaru 45 da yara biyu. Malami ne a fannin karatun aikin banki na jami’ar. An zargesa ne tare da kama shi da laifi daya tak na fyade.

Kamar yadda masu gabatar da kara wadanda suka samu jagorancin Yhaqub G. Oshoala suka sanar, tsohon malamin ya aikata fyaden ne ga yarinyar wajen karfe 9:25 na safiyar ranar 23 ga watan Yuli 2015 a daki mai lamba 8 na sashen da yake aiki a jami’ar.

Fyade: An yankewa malamin jami'a hukuncin shekaru 21 a gidan gyaran hali

Fyade: An yankewa malamin jami'a hukuncin shekaru 21 a gidan gyaran hali
Source: UGC

DUBA WANNAN: Muna bukatar karin sojoji 100,000 domin cin galaba a kan Boko Haram - Zulum

Oshoala, wanda shine shugaban hukumar gurfanarwa ya sanar da kotun cewa, wanda ya aikata laifin abokin mahaifin yarinyar ne kuma an bukacesa ne ya taimaka mata wajen samun gurbin karatu a makarantar.

Mai gabatarwar ya ce Baruwa yayi mata fyade ne lokacin da taje ofishinsa kuma hakan ya ci karo da sashi na 258 na dokokin jihar Legas na 2011.

Masu gabatar da karar sun bayyana shaidunsu gaban kotu inda suka gabatar da wacce aka yi wa fyaden, mahaifinta, likita da kuma dan sanda mai bincike.

Baruwa ya amsa laifinsa a ranar 31 ga watan Mayu na 2018 cewa yayi lalata da yarinyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel