An kama mutum biyu da ke yada bidiyon tsiraicin wata matar aure

An kama mutum biyu da ke yada bidiyon tsiraicin wata matar aure

A ranar Talata 19 ga watan Fabrairu ne jami'an 'yan sandan jihar Anambra suka gurfanar da wasu mutane biyu a kan zarginsu da laifin yada hotunan tsiraicin matar aure a Facebook.

Chigozie Agunwa mai shekaru 38 da kuna Ebele Uzor mai shekaru 30 an zargesu da wallafa bidiyon tsiraicin Mirabel Anedo a kafar sada zumuntar zamani. Lamarin ya faru ne watan Maris na 2019.

Da mai karar da wadanda aka yi karar duk suna zama ne a Onitsha, babban birnin kasuwancin jihar Anambra.

Wacce ta kai karar ta bayyana cewa ta manta bidiyon tsiraicin a wayarta ne kafin ta siyarwa da Agunwa wayar.

Daga baya kuwa ta ga bidiyonta na yawo a Facebook wanda Ogechi Okeke ya wallafa.

An kama mutum biyu da ke yada bidiyon tsiraicin wata matar aure

An kama mutum biyu da ke yada bidiyon tsiraicin wata matar aure
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Wutan lantarki ta kashe shugaban masu tsaron Rotimi Amaechi a Kaduna

Wata kungiyar rajin kare hakkin dan Adam mai suna Behind Bars Initiative ce ta mika koken ga hukumar 'yan sanda.

"Mun yi bincike sannan muka mika kokenmu ga kwamishinan 'yan sandan jihar Anambra. An kama mutane biyar amma an saki uku daga ciki. Wadanda aka sakin basu laifi din kallon bidiyon kadai suka yi. Basu yada shi ba," in ji Harrison Gwamnishu wanda ke jagorantar kungiyar.

Dan sanda mai gabatar da kara, Ikemefuna Nnamani ya sanar da kotun majistare din da ke Onitsha cewa laifinsu abin hukuntawa ne a karkashin dokokin jihar Anambra.

Agunwa da Uzor sun musanta laifinsu. An bada belin kowannensu a kan N100,000.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel