Bidiyon tsiraici: Deezell ya yi karar Maryam Booth da wasu mutane 6 a kotu

Bidiyon tsiraici: Deezell ya yi karar Maryam Booth da wasu mutane 6 a kotu

Mawakin Najeriya da ke zaune a Dubai, Ibrahim Rufai da aka fi sani da Deezell da ake zargin shine ya fitar da bidiyon tsiraicin jarumar Kannywood Maryam Booth a dandalin sada zumunta ya yi karar jarumar a kotu.

Mutane da dama sun yi ta maganganu a kan Maryam Booth bayan fitowar bidiyon da bisa ga dukkan alamu wani/wata na kusa da jarumar ne ya dauka.

Maryam ta wallafa rubutu inda ta yi zargin cewa tsohon saurayin ta Deezell ne ya nadi bidiyon.

Maryam ta rubuta a Instagram cewa, "A irin wannan yanayin, ya kamata mutum ya yi nazari kafin ya yi magana. Amma gaskiya ne Deezell wanda tsohon saurayi na ne ya lalabo ya dauke ni bidiyon lokacin ina canja kaya."

Jarumar ta rubuta cewa za ta yi kara a kotu domin a bi mata hakkin ta.

A bangarensa, Deezell bai yi wata-wata ba ya yi mata martani inda ya ce ba shine ya fitar da bidiyon tsiraicin ba a kafafen sada zumunta inda shi ma ya kara da cewa zai yi karar Maryam a kotu muddin ba ta janye zargin da ta masa ba kuma ta nemi afuwarsa cikin sa'o'i 12.

Daga bisani, mawakin ya yi karar jarumar a kotu inda ya ke zargin ta da bata masa suna, sharri da kazafi, zaginsa da ci masa mutunci da wasu laifukan.

DUBA WANNAN: Ya yi karar matarsa a kotu domin ta hana shi kusantar har tsawon kwanaki 48

Ya rubuta, "A farkon wannan makon, na fitar da sanarwar biyu inda na nesanta kai na daga zargin da ake min. Na kuma bukaci wadanda suka yi zargin su janye kuma su nemi afuwa ta. Wasu sun janye kuma sun nemi afuwa ta amma wasu ba su janye ba.

"Bayan tattauna wa da lauyoyi na na Amurka da na Najeriya, na dauki matakin shigar da kara a kotu na bata min suna, hadin baki da sharri, zagi da cin mutunci kamar yadda doka ta tanada.

"Kotu ta umurci rundunar 'yan sandan Najeriya ta gudanar da cikakken bincike a kan wadanda suka wallafa rubutu a kai na musamman na 3 zuwa 7 yayin da wasu da ba a ambaci sunansu ba suma za su gurfana a kotu. Sai mun hadu da ku a kotu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel