Bidiyon tsiraici: Kungiya ta kare Sanata Uba Sani

Bidiyon tsiraici: Kungiya ta kare Sanata Uba Sani

Wata kungiyar yada labarai mai suna Digital Home With Internal Solution tayi kira ga iyalan Sanata Uba Sani da 'yan uwansa a kan su kwantar da hankalinsu a kan bidiyon da ya fita. Kungiyar ta ce hatta 'yan Najeriya sun san cewa aikin makiya ne kuma mahassada, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

Kungiyar, wacce ta kwatanta aikin da na wadanda basu waye ba, ta kwatanta bidiyon da zama na bogi tare da cewa "da izinin Ubangiji zamu yi iya kokarinmu don ganin mun binciki lamarin."

Kamar yadda takardar da shugaban kungiyar ta kasa, Ambasada Ibrahim Bala Aboki yasa hannu, ya ce "sanannen abu ne idan aka ce ma'abota amfani da yanar gizo a Najeriya sun kware wajen yada labaran bogi da na kiyayya. Hakan kuwa ba dai-dai bane garemu."

Bidiyon tsiraici: Kungiya ta kare Sanata Uba Sani

Bidiyon tsiraici: Kungiya ta kare Sanata Uba Sani
Source: UGC

DUBA WANNAN: Zuciya: Dattijo mai shekaru 78 ya dawo gida bayan shekaru 26 da samun sabani da matarsa

"A don haka muke kira ga 'yan Najeriya da su gujewa yadawa tare da baza labaran bogi ballantana sakonni daga 'yan Najeriya mazauna ketare da kuma na gida.

"Labaran bogi ne da kuma munanan hotuna da aka hada don kokarin zubarwa Sanatan mutunci. DHIS na kira ga 'yan Najeriya da ke da dabi'ar yada sakonnin da suke tada zaune tsaye tare da kawo tashin hankali da su shiga taitayinsu. Wannan ba abu ne na kirki ba.

"Wannan bidiyon da ake yadawa wata hanya ce ta tada zaune tsaye kuma wasu masu son ganin sun kaishi kasa ne suka dau nauyin abin. Zamuyi duk abinda ya dace tare da jami'an tsaro wajen cafko wadanda suka yi wannan shirmen." Aboki ya kara da cewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel