An kama karuwai 37 a Jigawa

An kama karuwai 37 a Jigawa

Jami'an hukumar Hisbah a Jihar Jigawa sun kama wasu da ake zargin karuwai ne har mutane 32 a karamar hukumar Kazaure.

An kama karuwan ne bayan da wasu jami'an na hukumar Hisbah suka kai sumame a wani sannanen dandali da ake kira Gada Joint a karamar hukumar Kazaure misalin karfe 5 na asubahin ranar Talata 11 ga watan Fabrairu.

Kwamandan Hisbah na jihar, Malam Ibrahim Dahiru ya tabbatar da sumamen kuma ya bayyana cewa an kama maza uku yayin sumamen.

Ya kara da cewa an kuma kwace kwalaben giya 147 da buhu guda daya na kwallaben giya.

An kama karuwai 37 a Jigawa

An kama karuwai 37 a Jigawa
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Bidiyon mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna tana kashe gobara ya jawo cece-kuce

A wani rahoton, mun kawo muku cewa mummunar gobara ta tashi a wani sashi na filin sauka da tashin jiragen sama na Sam Mbakwe Intarnational Cargo da ke Owerri a jihar Imo, kamar yadda Sahara Reporters suka ruwaito.

Babbar manajar hukumar filayen sauka da tashin jiragen sama ta Najeriya, Henrietta Yakubu, ta ce gobarar ta barke ne sakamakon wutar daji da ta shafi filin jirgi. Yakubu ta ce a halin yanzu masu kashe gobara na kokarin ganin sun kasheta.

Hukumar filayen jiragen saman Najeriya na kira ga ma’aikatan filayen jiragen da su guji saka wuta a dattin da aka tattara a farfajiya ko kewayen filayen don hakan na kawo manyan kalubale.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel