Wasu mutane biyu sun raunta abokinsu da fasashiyar kwalba a kan karan tabar sigari

Wasu mutane biyu sun raunta abokinsu da fasashiyar kwalba a kan karan tabar sigari

A ranar Talata ne rundunar 'yan sandan Najeriya ta gurfanar da wasu mutane biyu a gaban wata kotun majistare da ke unguwar Wuse Zone 6 a Abuja bisa zarginsu da yin amfani da fasashiyar kwalba wajen raunata abokinsu a kan taba sigari.

Rundunar 'yan sanda ta gurfanar da mutanen; Gabriel Esezabar da Lawrence Mathew, bisa tuhumarsu da hada kai tare da raunata abokinsu.

Lauya mai gabatar da kara, Peter Ejike, ya sanar da kotun cewa wadanda aka gurfanar din sun aikata laifin ne ranar 6 ga watan Fabrairu.

Ya bayyana cewa tun a ranar wanda suka raunata, Moses Musa, mazaunin unguwar Wuse Zone 3, ya shigar da korafi a Ofishin rundunar 'yan sanda na unguwar Wuse Zone 3.

Ejike ya bayyana cewa Esezabar da Mathew sun raunata Musa da wata fasashiyar kwalba yayin da cacar baki ta barke a tsakaninsu a kan taba sigari filin shakata wa na unguwar Wuse Zone 3.

Wasu mutane biyu sun raunta abokinsu da fasashiyar kwalba a kan karan tabar sigarai

Taba Sigari
Source: UGC

Mai gabatar da karar ya ce laifin da mutanen da suka aikata ya saba wa sashe na 79 da na 245 na kundin aikata laifuka.

DUBA WANNAN: An kama babban sojan Najeriya da ya gudu a kasar Benin

Sai dai, a wani salo da ya bawa mutane mamaki, mai gabatar da karar ya shaida wa kotu cewa mai kara da wadanda ake kara sun cimma yarjejeniyar sulhunt wa da yin maslaha a wajen kotu

A saboda haka ne lauya Ejike ya cike tarkardar janye kara, watau FIR (First Information Report).

Alaklin kotun, Omolola Akindele, ya kori karar tare da sallamar masu laifin da aka gurfanar a gabansa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel