Tirkashi: An kama 'yan Chinese guda biyu da suka yi luwadi da wani dan Najeriya ta hanyar yi masa fyade

Tirkashi: An kama 'yan Chinese guda biyu da suka yi luwadi da wani dan Najeriya ta hanyar yi masa fyade

- Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta cafke wasu mutane biyu ‘yan asalin kasar China wadanda ake zargi da fyade

- Jun Lan-Yin yana zama tare da mutanen biyu ne amma ya kai korafin cewa suna luwadi da shi a yayin da yake bacci

- Kamfanin da suka baro a baya ya tabbatar da cewa ‘yan luwadi ne kuma binciken likita ya tabbatar da cewa suna lalata da abokin nasu

‘Yan sandan da suke aiki a yankin Area F na Ikeja da ke jihar Legas sun kama wasu mutane biyu ‘yan asalin kasar China. Yang Liang mai shekaru 41 da kuma Wang Gui mai shekaru 45 ana zarginsu ne da yi wa wani abokinsu fyade.

Jaridar vanguard ta ruwaito cewa wadanda ake zargin na yi wa Jun Lan-Yin fyade wanda abokinsu ne, kuma suna zama a daki daya ne a Morison Crescent da ke Ikeja a jihar Legas.

An gano cewa wandanda ake zargin da kuma wanda ake yi wa fyaden duk ma’aikata ne a Life Mate Furniture.

“A yayin bincike, an gano cewa wadanda ake zargin ‘yan luwadi ne tun a wajen aikinsu na farko. Wancan kamfanin da suka baro ya tabbatar da cewa suna luwadi,” wata majiya a cikin ‘yan sandan ta sanar.

KU KARANTA: Asirin fasto ya tonu, bayan wani mutumi ya bayyana yadda ya kama shi yana kwanciya da matarshi da kuma 'yarshi

Wanda ake yi wa fyaden da kanshi ya kai korafin su gaban ‘yan sandan tare da cewa suna shigar shi ta baya a yayin da yake bacci.

Bayan kai korafin da yayi, jami’an ‘yan sandan wadanda suka samu jagorancin ACP Olasoji Akinbayo, sun kama wadanda ake zargin.

Rahoton likita bayan ya kammala duba mai kai karar ya tabbatar da cewa ana shigar shi ta baya. An gano cewa wadanda ake zargin da kuma wanda ya kai karar duk suna rayuwa ne a Najeriya bayan Visa dinsu ta lalace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel