Daga karshe: Deezell yayi magana a kan bidiyon tsiraicin Maryam Booth

Daga karshe: Deezell yayi magana a kan bidiyon tsiraicin Maryam Booth

Matashin mawaki na Arewacin Najeriya mai suna Ibrahim Ahmad Rufai, wanda aka fi sani da Deezell, ya musanta zargin da aka masa na sakin bidiyon tsiraicin jaruma Maryam Booth.

Kamar yadda jaruma Maryam Booth ta wallafa a shafinta na tuwita, ta ce mawakin ne ya dauketa a yayin da take sauya kaya. Kuma wannan bidiyon yayi shekaru uku.

Jarumin bai yi kasa a guiwa ba ya fito tare da wallafa rubutu don wanke kansa daga zargin da ake masa. Ya wallafa rubutun ne da harshen turanci. Ga abinda ya ce:

"Hankalina ya kai ga wani bidiyon tsiraicin fitacciyar jaruma Maryam Booth tare da zargin cewa akwai hannuna a sakinsa. Amma kuma wadannan mabarnatan sun kasa fito da wata shaida wacce ke bayyana cewa ni ne na saki.

"Kamar yadda lamarin ke bukatar martani, ina son tabbatar da cewa bani da hannu cikin sakin bidiyon kuma ban san masu hannu wajen sakinsa ba.

Daga karshe: Deezell yayi magana a kan bidiyon tsiraicin Maryam Booth

Daga karshe: Deezell yayi magana a kan bidiyon tsiraicin Maryam Booth
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Bidiyon tsiraicin Maryam Booth: Gaskiya ta fara bayyana daga bakin shugabannin ‘yan fim

"A matsayina na musulmi, nasan cewa Qur'ani da sunnah basu yarje min yada aibun wani ba ballantana a kafar sada zumuntar zamani don tozarta shi. Wannan zargin da ake min karya ne kuma ina so in tabbatarwa da jama'a cewa babu gaskiya a cikinsa.

"Duk da cewa ban san dalilin wannan zargin ba, ina so inyi kira ga masu wannan zargin da su janye shi tare da bada hakuri a kafar sada zumuntar zamani cikin sa'o'i 12 daga yanzu. Rashin yin hakan zai tirsasa ni daukar matakin shari'a don kare martaba ta da sunana.

"Daga karshe ina jaje ga wacce abin ya faru da ita tare da kira gareta da ta bincika tushen bidiyon da kuma daukar matakin shari'a da ya dace."

Daga karshe: Deezell yayi magana a kan bidiyon tsiraicin Maryam Booth

Daga karshe: Deezell yayi magana a kan bidiyon tsiraicin Maryam Booth
Source: Twitter

Daga karshe: Deezell yayi magana a kan bidiyon tsiraicin Maryam Booth

Daga karshe: Deezell yayi magana a kan bidiyon tsiraicin Maryam Booth
Source: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.haus

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel