Ina busar iska zan saki bidiyon kaina tsirara - Nafisa Abdullahi

Ina busar iska zan saki bidiyon kaina tsirara - Nafisa Abdullahi

Bayan mganganu na nuna bacin rai da jaruma Nafisa Abdullahi tayi a shafinta na tuwita a kan cece-kucen da bidiyon Maryam Booth ya jawo, jarumar ta sha alwashin sakin nata bidiyon tsirara.

Tuna a jiya dai jarumar aka tunzurota bayan tayi magana kan cewa sun san wanda ya yada bidiyon kawarta, kuma sai yayi dana sani. Wani dai ma'abocin amfani da tuwita din yayi mata raddi da cewa ta rufewa mutane baki kafin ita ma a saki nata., lamarin da ya matukar tunzura jarumar ta fara zage-zage.

Tun daga wancan lokacin ne aka fara raddi da martani ga jarumar amma kuma wasu sai suka yi ta karfafa mata guiwa tare da kare ta.

Ina busar iska zan saki bidiyon kaina tsirara - Nafisa Abdullahi

Ina busar iska zan saki bidiyon kaina tsirara - Nafisa Abdullahi
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Bidiyon tsiraicin Maryam Booth: Gaskiya ta fara bayyana daga bakin shugabannin ‘yan fim

Ta wallafa cewa, "Idan kun ga dama kuyi ta jayayya har abada, na riga na fada abinda zan fada. babu abinda zaku ce da ba a taba yi ba. babu wani abu sabo. Ni matsalata daya ma lokacin da na sa gajerun wanduna ban kile ba. Ina ma yanzu ne, da an ga sura da iya gayu."

Ta kara da cewa, "Amma ko yanzu bata baci ba, duk lokacin da na bushi iska zaku ganni da bikini."

Bikini dai a hausance zamu iya kiransa da bireziya da dan kamfai wanda Turawa ke sakawa idan zasu shiga ruwa ko yayin shan iska. Za ka ga akasarin shi bireziyar bata rufe nono kuma dan kamfai din zare ne gareshi wanda baya ko rufe mazaunai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel