Bidiyon tsiraicin Maryam Booth: Gaskiya ta fara bayyana daga bakin shugabannin ‘yan fim

Bidiyon tsiraicin Maryam Booth: Gaskiya ta fara bayyana daga bakin shugabannin ‘yan fim

Mujallar fim ta ruwaito cewa, shugabannin masana’antar fina-finai suna taimakawa jami’an tsaro wajen kama wasu mutum biyu da aae zargi da fitar da wani bidiyon tsiraici na fitacciyar jaruma Maryam Booth tsirara tare da yada shi a soshoyal midiya.

Tun daga ranar Alhamis ne faifan bidiyon na takaitaccen sakanni ya fita. An fada wa mujallar fim cewa yau shekaru uku kenan da aka dau bidiyon.

A bidiyon mai tsawon dakika uku kacal, an ga kyakyawar jarumar tsirara tana fitowa daga bandaki babu komai a jikinta.

Akwai tabbacin cewa wanda ya dau bidiyon ya dauka ne ba tare da amincewarta ba, don kuwa tana ankara ana daukarta tayi wuf ta kwace wayar da ake daukar da ita.

Mujallar fim tayi kokarin jin ta bakin jarumar, amma wayarta na kashe. Sai dai shugaban kungiyar jaruman Kannywood ta jihar Kano, Malam Alasan Kwalle, ya tabbatar wa da mujallar cewa kungiyarsa ta shiga lamarin. Tana taimakawa wajen samun kama mutane biyu namiji da mace wadanda ake da tabbacin sune suka saki bidiyon a gari.

Bidiyon tsiraicin Maryam Booth: Gaskiya ta fara bayyana daga bakin shugabannin ‘yan fim

Bidiyon tsiraicin Maryam Booth: Gaskiya ta fara bayyana daga bakin shugabannin ‘yan fim
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Bidiyon tsiraicin wani Sanata: Kowa nayi, wasu sun fi wasu wayau - Sanata mai jaje

Mutum biyun sun jima suna cutar jarumar suna karbar kudi daga hannunta da barazanar cewa idan bata basu ba zasu saki biyon a gari, kamar yadda Alasan Kwalle ya sanar.

Amma abinda tashar tsakar gida ta bincika ta gano shine, wannan lamarin ya faru tun shekaru uku da suka gabata. Kuma mutane biyun sun dade suna karbar kudi daga hannun jarumar da barazanar zasu wallafa bidiyon idan bata bada ba..

A haka ne daya daga cikinsu ya tambayi jarumar kudi cikin kwanakin nan, a cewarsa zai kai mahaifiyarsa asibiti. Maryam ta ce bata da kudin, lamarin da yayi sanadiyyar fitar bidiyon.

Akwai shaidar banki wacce ta kunshi duk kudaden da ta dinga tura musu, don haka za a yi amfani da ita wajen hukuntasu bayan sun shiga hannu.

Shi kuwa sakataren kungiyar masu shirya fina-finai ta kasa (MOPPAN), Malam Salisu Muhammad Officer, da mujallar fim tayi mishi tambaya game da lamarin, sai yace “mun san da maganar, amma a matsayinmu na shuwagabannin harkar fim ba zamu shiga ba saboda rayuwarta ce.”

Wata kawar Maryam Booth ta sanar da mujallar fim cewa, al’amarin ya matukar girgiza jarumar don tayi ta kuka a kan wannan cin amanar da aka yi mata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel