Bidiyon tsiraicin wani Sanata: Kowa nayi, wasu sun fi wasu wayau - Sanata mai jaje

Bidiyon tsiraicin wani Sanata: Kowa nayi, wasu sun fi wasu wayau - Sanata mai jaje

Waye ke son ganin bayan Sanatan daga yankin Arewa maso yamma? Hotunan tsiraicin wani sanata sun bayyana bayan wata harkalla a boye da yayi.

Bayan kammala harkar, an ga bidiyon sanatan tsirara yana fitowa daga bandaki inda yake goge jikinsa da farin tawul. Mazakutarsa na rawa tamkar igiyar sakale mutum.

Duk da cewa Sanatoci da yawa basu samu ganin wannan bidiyon ba, ba su ga wani abin kunya da ya faru a cikin bidiyon ba, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Akasi da dalilin da yasa aka watsa bidiyon, Sanatan ba zai fuskanci wasu tambayoyi ba daga majalisar don da yawa daga cikin abokan aikinsa sun tausaya masa.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Bam ya tashi a gidan gwamnatin jihar Ekiti

A takaice dai, ya samu masu ziyartarsa don jajanta masa aukuwar lamarin. An ji daya daga cikin sanatocin na cewa: "Dukkanmu muna yi amma wasu sun fi wasu taka-tsan-tsan. Mun cika yarda da mutane. Ba zamu tuhumesa ba a kan rayuwarsa."

Tambayoyin da sanatocin ke da su sune: Waye ke son ganin bayansa? A kan me sanata zai bari a dau bidiyonsa tsirara? Anyi hakan ne don tashin burinsa na siyasa a 2023?

Babban abin tsoron da zai ta kai kawo a zuciyar sanatan shine, akwai yuwuwar wanda ya wallafa bidiyon na da wasu.

Cikin kwanaki kadan masu zuwa ne za a san matsayar sanatan majalisa karo ta tara din.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel