Kano: An samu gawar wani saurayi da budurwa tsirara cikin wani gida

Kano: An samu gawar wani saurayi da budurwa tsirara cikin wani gida

- An tsinci gawar wani saurayi da wata budurwa tsirara a cikin wani gida da ke yankin unguwar Badawa da ke jahar Kano

- Rundunar yan sandan jahar ta tabbatar da lamarin inda tace an tsici gawar ne a cikin dakin girki da ke gidan

- Zuwa yanzu dai ba a tabbatar da abunda ya haddasa mutuwar tasu ba, amma dai 'yan sandan sun ce suna kan gudanar da bincike a kan lamarin

Rahotanni sun kawo cewa an tsinci gawar wani saurayi da wata budurwa tsirara a cikin wani gida da ke yankin unguwar Badawa da ke jahar Kano.

Shafin BBC ta ruwaito cewa rundunar yan sanda reshen jahar ta tabbatar da samun gawar tasu tsirara a cikin dakin girki da ke gidan.

KU KARANTA KUMA: Budurwa ta firgita mutumin da zai yi mata fyade, bayan ta gaya masa cewa tana da cutar Corona

Sai dai kuma har yanzu ba a tabbatar da abunda ya haddasa mutuwar tasu ba, amma dai 'yan sandan sun ce suna kan gudanar da bincike a kan lamarin.

A wani labarin kuma, mun ji cewa Jami’an ‘yan sanda na runduna ta musamman a kan binciken laifukan kisa a jihar Legas sun bazama neman wani matashi mai shekaru 23.

An zargi Michael Okhide da sokawa mahaifinshi mai suna Barista Clement Okhide wuka tare da mahaifiyar shi wanda hakan yayi sanadin mutuwarsu har lahira.

An gano cewa matashin ya soka wa kanwar shi wuka a ciki da hannu kafin ya tsere, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Mummunan lamarin ya faru ne a ranar Talata, 4 ga watan Fabrairu 2020 a gida mai lamba 6 titin Akeen Gbadamosi da ke Ejigbo, a jihar Legas. An gano cewa, wanda ake zargin ya ajiye gawar mahaifin nashi a madafi ne yayin da ya kulle gawar mahaifiyar shi a wani daki a cikin gidan kafin ya gudu.

Wata majiya daga jami’an tsaron ta ce sunan mahaifiyar wanda ake zargin Toyin Okhide kuma tana da shekaru 50 ne a duniya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Newspaper

Online view pixel