Yan bindiga sun kashe mutane 3 a sabon harin da aka kai kan Kaduna

Yan bindiga sun kashe mutane 3 a sabon harin da aka kai kan Kaduna

- Mutane uku aka kashe sakamakon wani hari da yan bindiga suka kai kan masarautar Zangon Attakar da ke jahar Kaduna

- Yan bindigan sun kai harin ne a farkon ranar Laraba, 5 ga watan Fabrairu a karamar hukumar Kaura da ke jahar Kaduna

- Sai dai hukumomin yan sanda basu tabbatar da lamarin ba tukuna

Rahotanni sun kawo cewa akalla mutane uku aka kashe biyo bayan wani hari da yan bindiga suka kai kan masarautar Zangon Attakar da ke jahar Kaduna.

An tattaro cewa sun kai harin ne a farkon ranar Laraba, 5 ga watan Fabrairu a karamar hukumar Kaura da ke jahar Kaduna.

Sai dai hukumomin yan sanda basu tabbatar da lamarin ba tukuna.

Amma wani Shugaban al’umman Fulani a yankin ya bayyana cewa an kashe yan fadarsa biyu da wani matafiyi a harin.

KU KARANTA KUMA: Rundunar 'yan sanda ta kubutar da mutane 26 daga hannun masu garkuwa da mutane

Bafulatanin ya ce mutanen da aka kashe na raka wasu kayyaki ne a mota lokacin da yan bindigan suka bude wuta sannan suka kashe biyu daga cikin yan kasuwar a nan take.

A wani labarin kuma, mun ji cewa manyan hafsoshin tsaron kasa sun bayyana ma majalisar wakilai cewa akwai hannun kasashen waje a cigaba da ruruwar matsalolin tsaro a Najeriya, musamman matsalar ta’addanci da sauran kalubalen tsaro.

Daily Trust ta ruwaito manyan hafsoshin tsaron sun bayyana haka ne yayin wata ganawar sirri da suka yi da kwamitin tsaro ta majalisar wakilai, kamar yadda shugaban kwamitin, Babajimi Benson ya bayyana ma manema labaru.

Babajimi yace hafsoshin tsaron sun yi bayanai da dama game da tsaro, don haka akwai bukatar zama a tattaunasu daya bayan daya, muhimmi daga ciki shi ne akwai yiwuwar sa hannu daga kasashen waje a rikicin.

Haka zalika a cikin wata tattaunawa da babban hafsan Sojan kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya yi da majiyar Legit.ng, ya bayyana cewa manyan hafsoshin tsaron tare da majalisar dokoki sun amince da yin aiki tare don kawo karshen matsalar tsaro.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel