Budurwa ta firgita mutumin da zai yi mata fyade, bayan ta gaya masa cewa tana da cutar Corona

Budurwa ta firgita mutumin da zai yi mata fyade, bayan ta gaya masa cewa tana da cutar Corona

- Wata mata da akayi yunkurin yi wa fyade ta tsorata mutumin da ya nemi keta mata haddi ta hanyar tari

- Matar mai zama a kasar China ta ce wa mutumin ne jiya ta dawo daga yankin Wuhan kuma tana dauke da cutar Coronavirus

- Mutumin bai kyaleta haka ba don sai da yayi awon gaba da kudaden ta da suka kai pam 338

Wata mata ‘yar kasar China ta tsoratar da wani mutum da yayi yunkurin mata fyade ta hanyar sanar da shi cewa tana dauke da cutar Coronavirus. Ta yi tari tare da sanar da shi cewa ta dawo ne daga yankin Wuhan, kamar yadda jaridar Daily mail ta ruwaito.

‘Yan sanda sun sanar da cewa yana wanda ake zargin mai suna Xiao na da shekaru 25 ne. ya fada gidan matar ne a daren Juma’a a birnin Jingshan wanda ke kusa da Wuhan, kamar yadda ‘yan sanda suka sanar.

A lokacin da ya so lalata da ita, matar ta sanar da shi cewa, “Jiya na dawo daga Wuhan kuma an kebe ni ne saboda kamuwa da nayi da cutar Coronavirus.”

Matar mai suna Yi ta yi tari inda ta ture saurayin wanda ke kokarin shaketa da rufe mata baki. Amma bayan da ya ji cutar da take dauke da ita, yayi awon gaba da kudinta har pam 338.

KU KARANTA: Siyasar jihar Kano: An kama mawakin Kwankwasiyya da yayi wakar 'A wanki gara'

Lamarin ya auku ne a birnin Pingba da ke wajen Jingshan wanda ke da nisan tafiyar sa’o’i uku zuwa Wuhan.

Jami’an ‘yan sanda sun ce wani mai suna Xiao ya tashi babu kudi a tare da shi sai ya bazama don yin fashi. Bayan shigar shi wajen matar ne ya yanke hukuncin kwanciya da ita.

Yi ta kira ‘yan sanda bayan tafiyarshi, amma koda suka fara bincike sun kasa gano shi saboda kowa na rufe da fuskar shi. Daga bisani ne Xiao ya kai kanshi hannun ‘yan sanda tare da amsa laifin shi. A halin yanzu yana rufe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel