Yadda wata mata da datse mazakutar wani da ya yi yunkurin mata fyade

Yadda wata mata da datse mazakutar wani da ya yi yunkurin mata fyade

Wata mata 'yar kasar Pakistan ta datse mazakutar wani mutum da ta yi ikirarin ya yi yunkurin yi mata fyade kamar yadda yan sanda suka bayyana a ranar Talata.

Matar yar shekara 25 ta yi amfani da wuka ta kare kanta daga mutumin da ya fado gidanta da ke Punjab inji jami'in dan sanda Mohamed Ilyas.

Matar ta shaidawa 'yan sanda cewa ita kadai ne a gidan lokacin da mutumin ya shigo gidan ya nemi ya ci zarafin ta.

Matar da ruga da gudu cikin dakin girki da dako wuka da datse mazakutar mutumin a lokacin da ya ke yunkurin cin zarafin ta kamar yadda matar da faɗi.

Wata mata ta datse al'aurar wani da ya yi yunkurin mata fyade

Wata mata ta datse al'aurar wani da ya yi yunkurin mata fyade
Source: Twitter

DUBA WANNAN:

Mutumin mai shekaru 28 yana asibitin birnin Faisalbad ana yi masa magani amma da zarar ya samu sauki za a masa tambayoyi inji Ilyas.

Sau da yawa ana zargi wadanda aka yi wa fyade da cewa suna sake wa maza fuska sosai ko kuma a ce suna suka janyo wa kansu.

Mata da yawa ba su kai wa yan sanda rahoto idan an musu fyade saboda irin tsangwama da za a rika musu musamman a gari na masu ra'ayin mazan jiya irin Pakistan a cewar kungiyar wayar da kan mutane ta Aurat.

Mai ƙare hakkin mata, Farzana Bari ta ce, "Abu ne mai ciwo sosai. Mafi yawan lokaci kotu da mutane su kan daura wa matan laifi."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel