An saki muhimman bayanai a kan Samuel, matashin da ya yi yunkurin tayar da bam a Cocin Kaduna

An saki muhimman bayanai a kan Samuel, matashin da ya yi yunkurin tayar da bam a Cocin Kaduna

Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta bayyana bayanai a kan mutumin da aka kama da bam a cocin Living Faith da ke Sabon Tasha a yankin karamar hukumar Chikun ta jihar.

An bayyana sunansa da Nathaniel Samuel, mutum mai matsakaicin shekaru wanda 'yan sandan suka mika ga sashin binciken manyan laifuka don amsa tambayoyi.

An saki muhimman bayanai a kan Samuel, matashin da ya yi yunkurin tayar da bam a Cocin Kaduna

An saki muhimman bayanai a kan Samuel, matashin da ya yi yunkurin tayar da bam a Cocin Kaduna
Source: Twitter

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, hankula sun tashi ne bayan da wani mamban cocin ya ankarar da jami'an tsaro cewa ya ga wani mutum na dasa wani abu mai fashewa a yayin da ake bauta.

A nan ne aka tunkaresa tare da cafke shi kafin daga bisani a cire bam din a sannu.

An gano cewa, ba wannan ne karo na farko da wanda ake zargin ya fara zuwa cocin ba. Ya je cocin a makon da ya gabata amma sai aka kore shi.

An saki muhimman bayanai a kan Samuel, matashin da ya yi yunkurin tayar da bam a Cocin Kaduna

An saki muhimman bayanai a kan Samuel, matashin da ya yi yunkurin tayar da bam a Cocin Kaduna
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Kuma dai: Yawan alkalan kotun koli ya sake ragu wa zuwa 13

Ekpenyong Edet, wanda shine shugaban masu tsaron cocin ya tabbatar wa da manema labarai hakan a jiya Lahadi.

Ya ce an lura da wanda ake zargin a CCTV yana dauke da jaka har zuwa shigar shi wajen bauta.

"Ya samu nasarar shiga kuma har ya zauna. Daga baya ne aka zarge shi tare da bincikar jakar wacce aka samu abu mai fashewa a ciki," cewar Edet.

An saki muhimman bayanai a kan Samuel, matashin da ya yi yunkurin tayar da bam a Cocin Kaduna

An saki muhimman bayanai a kan Samuel, matashin da ya yi yunkurin tayar da bam a Cocin Kaduna
Source: Twitter

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Yakubu Sabo ya bayyanawa gidan talabijin din Channels cewa za a binciki Samuel a kan dalilin da yasa ya shiga wajen bautar da abu mai fashewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel