Matashi dan shekara 18 ya yiwa Kakarsa mai shekaru 70 fyade

Matashi dan shekara 18 ya yiwa Kakarsa mai shekaru 70 fyade

- Wani matashi mai shekaru 18 ya shiga hannun 'yan sandan jihar Filato a kan zargin shi da ake da yi wa kakarshi mai shekaru 70 fyade

- Matashin ya ce aikin shaidan ne don kuwa sha'awa ce wacce ya rasa yadda zai yi da kanshi ta dame shi

- Ya roki kakan shi da ya yafe mishi tare da dattijan kauyen bayan an mika shi ga 'yan sanda

Jami'an 'yan sanda a jihar Filato a ranar Juma'a sun kama wani matashi mai shekaru 18 mai suna Marvellous Luka. Ana zargin matashin ne da yi wa kakar shi mai shekaru 70 fyade, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Dan sandan da al'amarin ke hannun shi, Sifeta Mulleng Alex, ya ce Luka, wanda ke zama a kauyen Dangu-gu da ke karamar hukumar Ampang ta yamma za a gurfanar da shi a gaban kotu.

Dan sandan ya zargi cewa, matashin ya hari kakar tashi ne a dakinta yayin da take bacci.

"Sha'awa ce ta kama ni kuma na rasa yadda zanyi da kaina a lokacin. Shiyasa na yanke shawarar kwanciya da ita. Kakata ta dinga kukan neman taimako amma nafi karfinta don haka na yi abinda nake so.

KU KARANTA: Ganduje ne ya taimaka mini na lashe zabe - Dan Kwankwasiyya da ya kada Jibrin Kofa

"Tayi kokarin kama ni bayan na gama amma sai na gudu na koma kasuwa inda nake turin baro. Daga nan ne naga wasu mutane sun kama ni tare da mika wa 'yan sanda." In ji wanda ake zargi.

Ya kara da cewa, "aikin shaidan ne kuma ina so kakana da dattawan kauyenmu su yafe min."

Mary Samuel, wacce shaida ce a kan abinda ya faru, ta ce taji ihun kakar tana neman taimako amma ita lokacin taje diban ruwa a fanfo ne. "Na sha mamakin abinda na gani. Nayi kokarin kama shi amma sai ya gudu. Daga nan ne nayi ihu aka bi shi har kasuwa aka kama shi. Na dauki zani wanda ke yashe a kasa na suturta tsohuwar," ta ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel