Wata sabuwa: Mazaje na takura matayensu shayar da su nono a kasar Uganda

Wata sabuwa: Mazaje na takura matayensu shayar da su nono a kasar Uganda

- Wani sabon bincike ya bayyana cewa an gano mazan kasar Uganda na tirsasawa matansu masu shayarwa basu nononsu

- Kamar yadda mazan suka bayyana, ruwan nonon matan masu shayarwan na zama kariya daga cuta mai karya garkuwar jiki da kansa

- Tsoron ma'abota kiwon lafiya shi ne yadda jarirai zasu dinga kwasar cutaka daga yawun manyan iyayensu maza da ke shan nonon iyayen mata

Kamar yadda wani sabon bincike ya nuna, an gano cewa mazan kasar Uganda na tirsasa matansu shayar dasu nono.

Kamar yadda jaridar Gistmania ta ruwaito, Sarah Opendi, ministar lafiyar kasar ta yi wannan maganar a zauren majalisar kasar.

"Maza a yanzu suna daga cikin matsalolin mata a lokacin da suke shayarwa. Uwa na shayar da jariri, kai kuwa mahaifi na son sha. Suna cewa yana maganin cuta mai karya garkuwar jiki, kansa da sauransu. Duk zance ne."

Ta kara da cewa "maza yanzu sun dau al'adar son shan nonon matansu masu shayarwa. Hakan matsala ce ga matan da kuma jariran da ake goyo."

Wani binciken kwanan nan wanda jami'ar Kyambogo da ke Kampala tare da jami'ar Kent ta Birtaniya suka gudanar da tallafin Global Challenges Research Fund.

Jaridar The Guardian UK ta ruwaito cewa binciken da aka yi a kauyen Buikwe ya nuna cewa wannan al'adar ta fara zama cin zarafi da matsi ga matan aure masu shayarwa.

Wani mutum ya bayyana cewa: "Na san wasu mazan na yin haka, amma bamu taba tattaunawa a kan hakan ba. Hakan ke nuna cewa maza sun saba yi."

KU KARANTA: Samun waje: Wani almajiri da baya karbar sadakar da tayi kasa da naira 500

Peter Rukundo, babban malami a jami'ar Kyambogo wanda ya taimaka wajen yin binciken ya ce, "Wasu yankunan a nan sun yadda cewa shan nonon mace na kara musu lafiya kuma yana maganin cutuka irinsu HIV da kansa."

"Akwai rashin wayar da kan mutane game da wannan matsalar. Amma babbar matsalar shi ne bamu san yawan mazan da ke aikata hakan ba. Akwai bukatar mu binciko hakan."

Thomas, daya daga cikin mazan da ke wannan dabi'ar ya ce "gaskiya ina jin dadin sha don yana warware gajiya sosai bayan na dawo daga aiki. Ba za ta iya hana ni ba saboda akwai wuyar denawa. Idan mace ta hana, za a iya cin zarafinta a kan hakan. Babbar matsala ce."

Wata mata kuwa mai kishin mijinta cewa tayi, "ina tsoron mijina ya je wani waje ya nema idan ban bashi ba."

Masana kiwon lafiya kuwa suna kallon yuwuwar daukar cutuka ne ga jariran da ke shan yawun manyan mutane bayan sun gama tsotse nonon mahaifiyar.

"Tsorona shine yadda idan abun ya ci gaba zai zama wani sashi na al'adar yaranmu masu tasowa," Merritt ta ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel