Yadda matar aure da kwartonta suka fatattaki mai gida daga gidansa bayan ya kama su suna lalata

Yadda matar aure da kwartonta suka fatattaki mai gida daga gidansa bayan ya kama su suna lalata

A ranar Laraba ne wani dan kasuwa mai suna David Ishaku ya yi karar matarsa a gaban wata kotun gargajiya da ke zamanta a Nyanya a Abuja.

Ya bukaci kotun da ta raba auren da ke tsakaninsa da matarsa mai suna Lucia saboda yadda kwartonta ya fatattake shi daga gidansa bayan ya kama su dumu-dumu suna lalata.

Mai karar wanda ke zaune a Abuja ya ce: "Nayi tafiya ne amma ban sanar da matata cewa ina kan hanyar dawowa ba. Tarko na hada mata kuma ta fada. Matata ta kawo kwarto cikin gida na. Bayan na sauka ne na gansu babu zato balle tsammani."

Yadda matar aure da kwartonta suka fatattaki mai gida daga gidansa bayan ya kama su suna lalata

Yadda matar aure da kwartonta suka fatattaki mai gida daga gidansa bayan ya kama su suna lalata
Source: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan majalisa sun bawa hammata iska a kan rabon fatanya

"A lokacin da na kalubalance ta, sai kwarton ya hadu da ita suka yi min dukan tsiya. Na matukar fusata kuma na umarce ta da ta bar min gida na amma sai ta kwaso min komatsaina ta watso waje tare da garkame gidan," in ji shi.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa a lokacin da aka kira shari'ar, wacce ake karar ba ta kotun kuma bata turo dan sako don sanar da dalilin da ya hana ta zuwa kotun ba.

Alkalin kotun, Mai shari'a Shittu Mohammed, a hukuncinsa ya ce: "wannan ne karo na farko da wannan kotu ta fara sauraron shari'a amma wanda ake karar bai halarci kotun ba domin ta bayar da ba'asi. Amma kuma saboda adalci irin na kotu, an dage cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 3 ga watan Fabrairu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel