Na gwammace mijina ya dinga kwanciya da karuwai a titi da ace na rasa shi baki daya - Matar aure

Na gwammace mijina ya dinga kwanciya da karuwai a titi da ace na rasa shi baki daya - Matar aure

- A makon da ya gabata ne Sammie Ayoka Peters, matar babban mawaki Sir Shina Peter ta yi bikin murnar cikarta shekaru 60

- Ta bayyana sirrin aurenta da mawakin wanda suka yi kusan shekaru 40 a kan cewa hakuri da addu'a ce madogara

- Ta ce karuwai basu taba daga mata hankali ba don ta san maza sun saba cin amana kuma halinsu ne

Idan zamu tuna Sammie Ayoka Peters ta hada kayataccen bikin murnar zagayowar haihuwarta a Legas. A yayin da ta zanta a kan aurenta mai kusan shekaru 40 da mawakin mijinta, ta bayyana yadda zamansu yake.

Matar mawakin ta ce; "Na auri mawakin amma tun farko na san mata na son mawaka. Duk da akwai wahala, dadi, kalubale da komai haka na jure. Ban taba tunanin rabuwa ba kuma haka shima mijin nawa."

A lokacin da aka tambayeta ko matan da ke zarya tare da neman soyayyar mijinta sun taba ta ta wani fanni, sai ta ce: "Wannan abu bai taba aure na ta kowanne bangafe ba. Gara mijina ya bi karuwai da in rabu da shi gaba daya. Wannan ne matsayata tun bani da wayau. Ba wai ba mijina ko mazan wasu kwarin guiwa nake ba, amma wannan ya sa na zauna lafiya babu hawan jini. Ina addu'a kuma babu abinda zai raba ni da mijina.

"Na fahimce shi kuma muna kaunar juna tare da ganin mutuncin juna. Bai taba kawo wata cikin gidana ba. Ina son shi kuma zan ci gaba da son shi. Babu abinda zai rage soyayyar nan."

DUBA WANNAN: Tashin hankali: Saurayi yayi kokarin yankewa mahaifiyarsa gaba, saboda taje tana zina da wasu a titi

Ta bayyana cewa ta hadu da Sir Shina Peters ne lokacin da take da shekaru 21. Iyayensu na da kusanci kamar 'yan uwa.

Daga karshe ta shawarci mata ta yadda zasu zauna cikin farin ciki a aurensu ba tare da sun saka wa kansu hawan jini ba.

"Idan zaki yi aure, ki roki ubangiji hakuri. Ki mutunta mijinki koda yayi kuskure. Ki bashi abinci banda hayaniya. Idan kika fahimci cewa maza sun saba cin amana sai hankalinki ya kwanta. Koda yana cin amanarki, ki yi addu'ar kada ya tozarta ki kuma ya mutunta auren da ke tsakaninku." in ji ta.

Kamar yadda jaridar Gistmania ta ruwaito, matar ta shawarci mata masu bibiyar mazan aure. "Baku da tausayi kuma kuna kashe auren wasu mata saboda kudi. Kada ki kuskura ki sa wata kuka, ki bar mata mijinta kawai." Ta ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel