Yan sanda sun gurfanar da wani mutum a kotu kan satar ayaba a Abuja

Yan sanda sun gurfanar da wani mutum a kotu kan satar ayaba a Abuja

Rahotanni sun kawo cewa rundunar yan sandan Najeriya reshen Abuja ta gurfanar da wani mutum mai suna Enejo Isah a gaban kotu a yankin Mpape da ke birnin tarayyar kasar kan zargin satar ayaba da ta kai darajar naira miliyan 1.8.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ya ruwaito cewa ana zargin Enejo Isah, wanda ke zaune a unguwar Mpape, da laifin sata da kuma shiga gonar wani ba tare da izini ba.

Lauya mai shigar da kara M.M. Austin ya bayyana wa kotun cewa a ranar 11 ga watan Janairu ne Enejo mai shekara 26 ya shiga gonar ayaba mallakar Emmanuel Tanko, inda ya saci ayabar da ta kai darajar naira miliyan 1.8.

Ya kuma zargi Enejo da hada kai da wani mai suna Solomon, wanda yanzu haka ya tsere, wurin aikata laifin. Ya kuma ce Emmanuel ya kai rahoton lamarin ne ga ofishin 'yan sanda na Mpape.

Austin ya ci gaba da cewa laifin ya saba wa sashe na 97 da kuma 288 na kundin shari'ar manyan laifuka. Sai dai Enejo ya musanta zargin.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Gwamnan Bauchi ya sallami shugaban ma’aikatan gidan gwamnati

Mai Shari'a Salihu Ibrahim ya bayar da belin wanda ake zargi kan naira miliyan 1 tare da mai tsaya masa mutum daya, sannan ya dage sauraron karar zuwa 30 ga watan janairu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel