Annobar 'Lassa Fever': Mutane 29 sun mutu, 195 sun kamu a jihohi 11

Annobar 'Lassa Fever': Mutane 29 sun mutu, 195 sun kamu a jihohi 11

Cibiyar kula da barkewar cutuka ta Najeriya (NCDC) ta bayyana cewa an samu mace-macen mutane 29 da kuma wasu 195 da aka samu da cutar zazzabin Lassa a fadin jihohi 11 na kasar nan.

Daraktan cibiyar, Dr Chikwe Ihekweazu ya bayyana hakan ne a takardar da yasa hannu kuma ya fitar a ranar Asabar a garin Abuja. Ya yi bayanin cewa wannan kiyasin na ranar Juma'a ne 24 ga watan Janairu.

Ihekweazu ya ce an tabbatar da barkewar cutar kashi 89 cikin wadanda ake zargi a jihohin Ondo, Edo da Ebonyi.

Shugaban ya ce a mayar da martanin cigaba da barkewar cutar zazzabin Lassa a jihohin kasar nan, NCDC ta bude layin gaggawa a ranar Juma'a don daukar matakin gaggawa.

Annobar 'Lassa Fever': Mutane 29 sun mutu, 195 sun kamu a jihohi 11
Annobar 'Lassa Fever': Mutane 29 sun mutu, 195 sun kamu a jihohi 11
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Zaben maye gurbi a Sokoto: Jama'a sun yi tururuwar fito wa domin kada kuri'a

Ihekweazu ya ce layikan gaggawan sun hada da na NEMA, ma'aikatar noma da raya karkara, WHO, UNICEF da wasu cibiyoyin lafiya na Amurka.

Ya ce NCDC din za ta cigaba da tallafawa jihohin da wannan cutar ta fada. Ya ce hukumar ta tura rundunar taimakon gaggawarta zuwa jihohi biyar da aka fara samun barkewar cutar.

Kamar yadda daraktan ya sanar, ministan lafiya, Dr. Osagie Ehanire ya jagoranci wasu wakilai zuwa jihar Kano a ranar Asabar bayan mutuwar wasu ma'aikatan lafiya biyu sakamakon cutar.

Hukumar ta kara inganta sadarwa tsakaninta da yankunan da cutar ta fara bullawa tare da tabbatar da wayar da kai ga jama'a a kan hanyoyin gujewa cutar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel