Za a kafa dokar tilastawa masu yiwa mata fyade su dinga aurensu

Za a kafa dokar tilastawa masu yiwa mata fyade su dinga aurensu

- Kasar Turkiyya za ta kirkiro da wata sabuwar dokar da za ta tilasta wa namijin da yayi wa karamar yarinya fyade aurenta

- Za a gabatar da dokar ne a majalisar kasar Turkiyya din a karshen wannan watan

- Sai dai kuma masu rajin kare hakkin mata sun kalli hakan a wata sabuwar hanya ta halasta auren yara da ci gaba da yi musu fyaden

Kasar Turkiyya za ta kirkiro da wata sabuwar doka a kan masu yi wa kananan yara fyade. Dokar za ta tilasta wa wadanda suka yi wa yaran kanana fyade aurensu.

Wannan sabuwar dokar da kasar ke son kirkirowa za ta kawo karshen daurin da ake yi wa maza masu yi wa kananan yara fyade. Matukar suka auri yaran, toh sun tsallake hukuncin shari'a.

Za a gabatar da dokar auren wanda aka yi wa fyaden ne ga majalisar kasar Turkiyya din a karshen watan nan kamar yadda jaridar Gistmania ta ruwaito.

KU KARANTA: An kama mai daukar hoto da ya yiwa dalibai bidiyo tsirara ya sanya a kafar sadarwa

Amma kuma sabuwar dokar da za a kirkira ta jawo cece-kuce a wajen masu rajin kare hakkin mata wadanda suke ganin hakan sabuwar hanya ce ta halasta cin zarafin yara tare da yi musu auren wuri. Hakan kuma na nufin za a ci gaba da yi musu fyaden bayan an auresu.

Makamanciyar wannan dokar ta kasa tabbatuwa a majalisar kasar bayan duniya ta yi caa a kansu a shekarar 2016.

Dokar kuma za ta rangwantawa maza matukar suka yi jima'i da yaran ba tare da yi musu ta karfi ba ko kuma wata barazana ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel