An kama mai daukar hoto da ya yiwa dalibai bidiyo tsirara ya sanya a kafar sadarwa

An kama mai daukar hoto da ya yiwa dalibai bidiyo tsirara ya sanya a kafar sadarwa

- Wata kotun majistare da ke Accra ta yankewa wani dan jarida hukuncin watanni shida a gidan yari tare da tara kala-kala

- Dan jaridar ya amsa laifinshi na wallafa bidiyon tsiraicin wata budurwa bayan ya dinga yi mata barazana yana karbar kudi a hannunta

- Bayan ya wallafa, ta same shi amma sai ya bukaci karin kudi don ya ciresu daga yanar gizon

Wata kotun majistare da ke Accra ta yankewa wani dan jarida hukuncin zaman gidan yari saboda wallafawa tare da siyar da bidiyon batsa.

A wani rahoton da Adomonline.com ya fitar, wata kotun Kaneshie ta umarci Richmond Clement Kobina Abegya da ya biya tarar cefa 4,800 ko kuma yayi zaman gidan yari na watanni shida.

Kamar hakan bai isa ba don kotun ta umarci Abegya da ya biya wacce ke cikin bidiyon cefa 5,000 zuwa ranar 3 ga watan Maris na wannan shekarar.

An zarge shi ne da wallafa bidiyon wata daliba na tsiraici bayan ya karba dumbin kudade daga hannunta. Mai shari'a Rosemond Dodua Agyiri ne ya yanke mishi hukuncin bisa rangwame.

Dan sanda mai gabatar da kara, ASP Sylvester Asare ya sanar da kotun cewa dalibar da ta kawo koken na zama ne a Tema yayin da Abegya ke zama a yanki na hudu na Tema.

KU KARANTA: Duk macen da bata son kudi ba macen aure ba ce - Reno Omokri

Ya yi bayanin cewa, a watan Yuli na shekarar da ta gabata, wanda aka yankewa hukuncin ya hadu da mai koken ne a WhatsApp inda suka zama abokai.

Wanda aka yankewa hukuncin ya fito ne a matsayin mace kuma ya bukaceta da ta tura mishi hoton tsiraicinta. Bata yi sanya ba ta tura amma daga baya sai ta gane namiji ne.

A nan ya dinga mika bukatar shi ta kudi wajenta tare da barazanar zai wallafa bidiyon matukar bata bada kudin ba. Ta dinga tura kudaden don rufuwar asirinta amma daga baya sai da ya wallafa.

Daga nan ne ta tunkare shi amma sai ya bukaci karin kudi don ya ciresu. Bayan ta bada ne ya ki cirewa. Lamarin da yasa ta mika kokenta ga hukumar 'yan sandan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel