Wasu kananan yara yan kasar Nijar sun yi mutuwar ban mamaki a jahar Kaduna

Wasu kananan yara yan kasar Nijar sun yi mutuwar ban mamaki a jahar Kaduna

Al’ummar yankin kasuwar barci na jahar Kaduna sun shiga halin jimami bayan gano gawarwakin wasu kananan yara guda biyu yan asalin kasar Nijar daga cikin shagon da suke kwana a kan titin Ibrahim Taiwo, Sabon Gari Tudun Wada Kaduna.

Daily Trust ta ruwaito lamarin ya gigita mazauna unguwar matuka musamman a loakcin da aka fitar da gawar yaran biyu daga cikin shagon da suke kwana da misalin karfe 6 na safe, sai dai an rasa dalilin mutuwarsu, amma wasu na danganta hakan gab akin hayakin dake tashi daga rishon girki da suke amfani da shi.

KU KARANTA: Ba duka aka lalace ba: An karrama Dansandan da bai taba amsan cin hanci ba

Tabbas an ga rishon girkin a cikin shagon, kuma shagon ba shi da wani taga da hayakin zai dinga fita, don haka ake kyautata zaton bakin hayakin rishon ne yayi sanadiyyar ajalinsu, amma dai Allah kadai Ya barma ba kansa sani.

Wani makwabcin mamatan mai suna Kabiru dake sayar da kayan gwanjo ya bayyana cewa sai da aka balla kofar shagon aka ya dauko gawarwakin. “Yaran biyu yan Nijar ne, kuma an tsinci gawarsu a cikin shagonsu. A nan suke sayar mana da shayi kullum a kasuwa, da idanuwa naga gawarwakinsu bayan an balla shagon.

“Muna zargin hayakin risho da suke amfani da shi wajen dafa ruwan shayi da suka ajiye a cikin shagon ne ya sanadiyyar mutuwarsu. Don shagon ya cika da hayaki a lokacin da makwabta suka balla kofar bayan sun lura yaran basu tashi sun fara sayar da shayi kamar yadda suka saba ba.” Inji shi.

Majiyarmu ta ruwaito tuni aka mika gawarwakin zuwa ofishin kungiyar yan kasar Nijar mazauna Najeriya domin a yi musu jana’iza.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel