ABU Zaria ta yi sabon shugaba

ABU Zaria ta yi sabon shugaba

- Hukumar gudanarwa ta jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a ranar Laraba za ta sanar da wanda zai zama sabon shugabanta jami'ar

- Kamar yadda wakilin jaridar Daily Trust ya bayyana. a halin yanzu kwamitin na Arewa House inda suke tantancewa 'yan takarar

- Akwai yuwuwar da yammacin yau Laraba din nan hukumar ta sanar da wanda zai maye gurbin Farfesa Abdullahi Garba

Hukumar gudanarwa ta jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a ranar Laraba za ta sanar da wanda zai zamo sabon shugaban jami'ar. Bayan kammala tattaunawa da dukkan masu neman kujerar, hukumar gudanarwar na dubawa tare da tantancewa, kuma akwai yuwuwar su sanar da wanda zai gaji Farfesa Ibrahim Garba.

Da wannan cigaban, za a kammala duk wasu matakai na samar da sabon shugaban jami'ar a yau din nan Laraba. Wakilin jaridar Daily Trust a Zaria na kula da wannan cigaban da ke faruwa a Arewa House da ke Kaduna inda ake tantancewar kuma 'yan kwamitin na tattaunawa.

Farfesoshi 18 ne aka bayyana a cikin jerin wadanda ke neman kujerar a taron ranar 6 ga watan Janairu, amma daga baya sai suka koma 11. Bakwai daga cikin masu neman kujerar sun janye da kansu ko kuma an ciresu ne saboda yawan shekarunsu.

DUBA WANNAN: An damke wani kwarto da ke sanya kayan mata yana zuwa gidan matan aure suna zina (Hotuna)

Farfesa Ibrahim Mu'uta ne na farko da ya janye sai Farfesa Doknan Decent Danjuma Shemi da Abubakar Sani Sambo. Daga cikin wadanda aka cire saboda shekaru sune Farfesa Zakari Mohammed, Shafiu Abdullahi da Nuhu Mohammed Jamo.

Farfesa Musa Hassan kuwa an cire shi ne saboda bai kai shekaru 10 da zama farfesa ba, Daily Trust ta gano. Farfesa Lawal Saidu, Sadiq Zubairu Abubakar, Kabiru Bala, Ezzedeen M. Abdulrahman, Abdullahi Mohammed duk sun halarci tantancewar.

Sauran sun hada da Farfesa Kabir Sabitu, Isa Marte Hussaini, ABdullahi A. Umar, Ibrahim Musa Umar, Idris Isa Funtua da Sani Ahmed Miko, jaridar Daily Trust ta gano.

Bayan tantancewar ne kwamitin gudanarwan ta bayyana Farfesa Kabiru Bala na bangaren gine-gine a matsayin sabon shugaban jami'ar da zai maye gurbin Farfesa Ibrahim Garba Riruwai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel