Makiyaya guda 4 sun yiwa wasu mata guda 4 fyade a lokaci daya

Makiyaya guda 4 sun yiwa wasu mata guda 4 fyade a lokaci daya

- A ranar Talata ne 'yan sanda suka damke wasu matasan Fulani makiyaya hudu da suka yi wa kananan yara fyade har da 'yar shekaru hudu

- Yaran sun ce matasan sun kamasu tare da musu mugun duka sannan suka yi musu fyade daya bayan daya

- Daya daga cikin wadanda ake zargin ya ce sha'awarsu ce ta motsa kuma basu da wajen sauketa shiyasa suka fada wa yaran

A ranar Talata ne 'yan sanda suka damke wasu makiyaya masu suna; Hamisu Mohammed mai shekaru 18, Rayanu Mohammed mai shekaru 15, Mustapha Yunusa mai shekaru 15 da Abbas Salisu mai shekaru 17, a kan zarginsu da ake da yi wa yara kanana fyade har da mai shekaru hudu.

Wadanda ake zargin duk 'yan kauyen Manger ne da ke karamar hukumar Bokkos da ke Filato, kamar yadda jaridar Pulse ta ruwaito.

Sashin bincike na musamman na rundunar 'yan sandan jihar ne suke damke dasu a halin yanzu.

Takardar zargin ta bayyana cewa a lokacin da makiyayan suke kiwon shanunsu ne suka ci karo da yaran. A nan ne suka yi wa yaran fyade.

Kamar yadda daya daga cikin wadanda abin ya faru dasu ta ce, suna komawa gida ne lokacin da matasan Fulani din suka tsaresu da sanda tare da dukansu.

KU KARANTA: Tashin hankali: Tsananin sanyi na kashe mutane a kasar Afghanistan

Lokacin da suka nemi guduwa ne matasan suka tsaresu tare da yi musu fyade.

Ta ce bayan fyaden ne suka hanzarta zuwa kauyen Luwapam da ke kusa inda suka nemi taimakon jama'a har aka kama su.

A kalaman matasan, sun amsa laifinsu kuma sun ce hada baki suka yi don yi wa yaran fyade.

Daya daga cikin wadanda ake zargin mai suna Hamisu Mohammed ya ce, "muna ganin yaran ne sha'awarmu ta tashi amma babu abinda zamu iya don kwantar da ita. A take kuwa muka yanke shawarar yi musu fyade."

Dan sanda mai gabatar da kara Sifeta E.A Inegbenoise ya tabbatar da kamen kuma ya ce nan ba da dadewa ba zasu bayyana gaban kotu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel