Yadda Fasto ya tunzura budurwa za ta kashe kanta, bayan ya wallafa hotunanta tsirara a soshiyal midiya

Yadda Fasto ya tunzura budurwa za ta kashe kanta, bayan ya wallafa hotunanta tsirara a soshiyal midiya

- Da kyar aka shawo kan wata budurwa mai suna Rita Abang bayan da ta yi yunkurin kashe kanta

- Fasto Francis Moses ne ya wallafa hotunanta tsirara a wata mahada ta cocinta da ke manhajar WhatsApp

- Wata kawarta ta bayyana cewa an samo kwalabe hudu na mummunar gubar Sniper a dakinta

Da kyar aka hana wata budurwa 'yar Najeriya daga kashe kanta bayan fasto ya wallafa hoton tsiraicinta a wata mahadar mutanen cocinsu dake amfani da manhajar WhatsApp.

An zargi cewa faston cocin Living Faith Church ne wanda aka fi sani Winners Chapel da wallafa hoton budurwar tsirara.

Budurwar ta rubuta wasiyyar karshe a shafukanta na tuwita da Facebook tare da WhatsApp. Ta kuma siyo kwalabe hudu na gubar nan ta maganin kwari mai suna Sniper, a rahoton da Jaridar Daily Gossip tayi.

Rita Abag ta rubuta; "Nasan kashe kai bashi da kyau amma bani da wata mafita da ta wuce hakan. Ina kaunar iyayena da diyata. Zuwa gobe zan kashe kaina. Ku sani cewa Francis Moses Ukugha ne ke da laifi. Ta yaya zai tozarta ni ta hanyar wallafa hotunan tsiraicina?"

KU KARANTA: Asiri ya tonu: 'Yan sanda na sayarwa da matsafa masu laifi kan kudi N80,000

Wata ma'abociya amfani da kafar sada zumuntar zamani ta tuwita mai suna Pricelesscindy ta tabbatar da cewa an samu tseratar da matar daga kashe kanta kuma a halin yanzu 'yan uwanta na lura da ita.

Ta wallafa: "Chioma babu wanda ke wasa da kashe kanshi, kamar yadda kawata ta wallafa cewa za ta kashe kanta jiya a tuwita, Facebook da WhatsApp. A halin yanzu 'yan uwanta na kusa suna lura da ita bayan an binciko kwalabe hudu na mummunar gubar Sniper a dakinta."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel