Tsananin sanyi ya sanya yanzu bama samun kasuwa - Karuwan jihar Kano sun koka

Tsananin sanyi ya sanya yanzu bama samun kasuwa - Karuwan jihar Kano sun koka

- Karuwai a jihar Kano sun koka da yadda yanayin sanyin nan ya rage musu kasuwa

- Wata karuwa mai suna Blessing O. 'yar asalin jihar Binuwai ta ce bata samun kudi kamar da saboda mutane basu fitowa sosai da dare

- Ta bayyana cewa ko kwanan gida a halin yanzu bata cika samu ba wanda yafi kawo mata kudi don namijin kan yi abinda yake so har cikin dare

Karuwai sun koka a kan yadda sanyi ke tilasta su zaman gida wanda hakan ke sa su rasa kwastomomi masu lalata dasu su biya kudi.

Wasu daga cikin karuwan da suka tattauna da jaridar Tribune Online sun ce yanayin sanyin nan ya rage musu yawan masu biyan kudi su kwanta dasu.

Wata mai suna Blessing 'yar asalin jihar Binuwai ta sanar da jaridar Tribune Online a titin Enugu da ke Sabongari a jihar Kano cewa bata samun kudi yanzu. Amma lokacin da ba na sanyi ba tana samun daga 8,000 zuwa 10,000 a daukan da ba na kwana ba.

KU KARANTA: Budurwa ta bayyana yadda mahaifinta ke bata naira dubu 60 a duk lokacin da yayi zina da ita

Amma ta ce wannan bai hada da kudin kwana ba saboda a kan kara mata 5,000 zuwa 10,000 a kan kudin matukar tare zata kwana da namijin kuma zai yi komai son ran shi.

"Amma wannan sanyin ya saka mu cikin wani hali. Na kan koma gida da N4,000 ko N6,000 a daukan da ba zan kwana ba kuma sau da yawa yanzu an dena daukana kwanan gida."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel