Rushewar gidan sama mai hawa 3 ya rutsa da wani mutumi a Legas

Rushewar gidan sama mai hawa 3 ya rutsa da wani mutumi a Legas

Wani gidan sama mai hawa uku ya rushe a kan titin Alasepe dake cikin unguwar Okota na jahar Legas, kuma ya danne wani mutumi da ba’a san ko wanene ba har zuwa lokacin tattara wannan rahoto.

Gidan talabijin na Channels ta ruwaito babban daraktan hukumar bada agajin gaggawa na jahar Legas, Oluwafemi Oke ya tabbatar da aukuwar hadari a ranar juma’a, inda yace suna ta kokarin gano mutumin da ginin ya danne.

KU KARANTA: Nan bada jimawa ba gwamnatin Najeriya za ta tura wakilinta zuwa duniyar wata

Rushewar gidan sama mai hawa 3 ya rutsa da wani mutumi a Legas

Rushewar gidan sama mai hawa 3 ya rutsa da wani mutumi a Legas
Source: Facebook

Bugu da kari, Mista Oke yace rushewar gidan saman ya tabi sauran gidajen dake makwabtaka da shi, don haka yace da zarar sun kammala aikin ceto wannan mutumi, zasu rusa sauran sassan gidan da bai gama rushewa ba.

“Isan mu wurin keda wuya sai muka tarar gidan daya fadi wani gidan sama ne mai hawa uku da aka kusan kammala aikin sa, amma akwai wani babban mutum namiji da ginin ya rutsa da shi, kuma tuni mun fara aikin ceto shi.

“Rushewar ginin ya yi tasiri a kan sauran gidajen dake gefensa, don haka muka takaita cikowar jama’an dake taruwa suka kallo. A yanzu haka muna amfani da dukkanin kayan aikin da muke dasu wajen ganin mun ceto wannan mutumi.” Inji shi.

A wani labarin kum, gwamnan jahar Katsina, Malam Aminu Bello Masari ya rattafa hannu kan wata sabuwar dokar hana zirga zirga acaba a garuruwan jahar Katsina gaba daya tun daga karfe 7 na dare zuwa karfe 6 na safiya.

Kwamishinan sharia na jahar ya bayyana cewa dokar za ta fara aiki ne daga ranar 20 ga watan Janairun shekarar 2020, sai dai yace dokar ba za ta yi aiki a kan jami’an hukumomin tsaro ba da suka hada da Sojoji, Yansanda, Civil Defense, kwastam, NDLEA da sauransu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel