Budurwa ta bayyana yadda ta sayar da budurcinta kan kudi Naira miliyan 473 a yanar gizo

Budurwa ta bayyana yadda ta sayar da budurcinta kan kudi Naira miliyan 473 a yanar gizo

- Wata matashiya mai shekaru 19 tayi ikirarin cewa zata siyar da budurcinta

- Wani dan kasuwa dake Munich ne ya taya kuma sun daidaita zai siya a kan N473,000,000

- Dan kasuwar yace zai dau nauyin yarinyar tare da aurenta nan gaba

Wata matashiya mai shekaru 19 tayi ikirarin cewa ta siyar da budurcinta a kan fam miliyan daya (£1m) wanda yayi dai-dai da N473,000,000. Budurwar tace ta siyar da budurcin nata ne ga wani babban dan kasuwar birnin Munich dake kasar Jamus ta hanyar wata kafar sada zumuntar zamani kuma yace a shirye yake don aurenta.

A watan Disamba ne budurwar ta bayyana cewa ta shirya siyar da budurcinta wanda wani cikakken likita ya tabbatar da shi.

KU KARANTA: Saurayina ya sayar dani ga wasu mutane N300,000 domin su dinga iskanci dani

A wannan makon ne kuwa kafar sada zumuntar zamanin ta tabbatar da cewa matashiyar ta shirya tsaf don siyarwa dan kasuwar mai shekaru 58 budurcinta. Dan kasuwar ya mallaki kadarori masu tarin yawa a Turai. Katya wacce take jin turanci da yaren kasar Rasha, tace zata kashe kudin ne ta hanyar yawon zagaya duniya da rayuwa mai cike da hutu da jin dadi.

Kamar yadda kafar sada zumuntar ta bayyana, mai siyen budurcin yace a shirye yake don auren Katya kuma zai dau dawainiyarta ta kudi. A duk watan duniya zai dinga bata Euro 10,000.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel