Matar da mijinta ya ya yankewa nonuwa ta bukaci ya dawo gareta ta yafe masa

Matar da mijinta ya ya yankewa nonuwa ta bukaci ya dawo gareta ta yafe masa

- A halin yanzu wata mata mai suna Lucy Moraa 'yar asalin Najeriya na fama da raunikan da mijinta Ephraim ya ji mata

- Ephraim ya caccakawa Lucy wuka a gabanta da nonuwanta ne bayan ta hana shi kudin da zai siya giya

- Lucy tace ya saba cin zarafinta amma a halin yanzu tana son shi kuma idan ya bata hakuri zata yafe mishi su koma zamansu lafiya

Wata mata mai suna Lucy Moraa wacce a halin yanzu take jinyar raunikan da mijinta ya ji mata tana rokon shi da ya dawo. Ephraim Malenge ya caccaki matar shi ne da wuka a gabanta da nonuwanta sakamakon fadan da ya hada su.

A yayin bayanin yadda lamarin ya faru, Lucy mai shekaru 31 tace mijinta ya ji mata raunin ne bayan ta hana shi kudin siyan giya. Mahaifiyar yara biyun ta sanar da gidan talabijin na K24.

"Yazo gida kuma ya karba Ksh40 duk da na sanar da shi cewa bani da kudi. Ya ja kunne na a kan zai ciremin kai yayi yawo dashi a titi. Zatona wasa yake yi amma dai na bashi kudin.

KU KARANTA: Tirkashi; Fasto ya damfari wata mata miliyan 36 akan cewa zai cire mata aljanu

"Ya tafi amma sai ya dawo babu dadewa. Ya ganni da jakar da nake aje kudi sai ya nemi kwacewa. Na sanar dashi cewa kudin makarantar 'ya'yanmu ne amma sai hakan ya fusata shi. A take ya dauko wuka ya caccaka min a gabana da nonuwana.

"Mun saba fada mu shirya daga bisani. Amma yanzu yaki dawowa. A shirye nake da in karbe shi idan ya dawo. Ina son mijina duk da yayi kokarin kasheni da yarona.

Lucy, wacce ta tabbatar da cewa Ephraim ya saba cin zarafinta, tace taki sanar da 'yan sanda ne saboda kada a kama mijinta masoyinta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel